Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Eid al-Fitr: Hotunan bikin Sallah a wasu ƙasashen Afirka

An gudanar da Sallar Idi a ƙasashen duniya, inda al'ummar Musulmi suka yi bukukuwa don nuna farin ciki da ƙulla zumunci. Musulmai a faɗin Afirka da ma duniya gabaɗaya sun gabatar da Sallar Idi, kuma suna ci gaba da shagulgulan Eid al-Fitr, wadda ranar biki ce da ke zuwa bayan watan Ramadana. Ana...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:10
Eid al-Fitr: Hotunan bikin Sallah a wasu ƙasashen Afirka
En bref

An gudanar da Sallar Idi a ƙasashen duniya, inda al'ummar Musulmi suka yi bukukuwa don nuna farin ciki da ƙulla zumunci. Musulmai a faɗin Afirka da ma duniya gabaɗaya sun gabatar da Sallar Idi, kuma suna ci gaba da shagulgulan Eid al-Fitr, wadda ranar biki ce da ke zuwa bayan watan Ramadana. Ana...

An gudanar da Sallar Idi a ƙasashen duniya, inda al'ummar Musulmi suka yi bukukuwa don nuna farin ciki da ƙulla zumunci. Musulmai a faɗin Afirka da ma duniya gabaɗaya sun gabatar da Sallar Idi, kuma suna ci gaba da shagulgulan Eid al-Fitr, wadda ranar biki ce da ke zuwa bayan watan Ramadana. Ana gudanar da shagulgulan ne tare da iyali, da haɗuwa da dangi, da kuma sanya sabbin kaya da cin kayan maƙulashe. Al'ummar Musulmi sun gabatar da Sallar Idi a filaye da masallatai, da ma kan tituna da harabobin masallatai. Wani ɗan sandan tarayya a tsaye lokacin gabatar da Sallar idi a filin wasa na Addis Ababa Stadium a birnin Addis Ababa. A Chadi, sojoji sun bar motocinsu suka ajiye makamansu don gabatar da Sallar idi tare da sauran Musulmai a safiyar ranar idi. Sojojin Chadi sun halarci filin idi a Espace Public in Adre A babban birnin Kenya, Nairobi, taron masallata sun haɗu a filin da ke yankin Ngara don gabatar da sallar idi. Masallata mata suna gabatar da Sallar idi a filin Sir Ali Muslim Club Ground, a Nairobi, Kenya. Masallata suna sallar idi a filin Sir Ali Muslim Club Ground a gundumar Ngara ta Nairobi, Kenya. A ƙauyen Abu Sir na yankin Giza a Masar, mutane sun fito da balo mai kalar tutar Falasɗinu suka taru don gabatar da addu'o'i na neman zaman lafiya a Falasɗinu, kamar yadda suka ambata. Yara mata Musulmai a Masar sun ɗauki hoto yayin da suke bikin Sallar Idi a ƙauyen Abu Sir, a Giza. “Barka da Sallah, ina fatan kwanakin da ke tafe na farin ciki ne. Allah ya taimaki 'yan uwanmu a Falasɗinu kuma ya kare su. Kuma, insha Allahu za su yi Idi cikin aminci da rahama.” cewar Abdallah Mohamed. Wani mutum yana ɗaga tutar Falasɗinu a filin idi na ƙauyen Abu Sir.