Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

ECOWAS na taro kan Nijar, Mali, Burkina Faso da Senegal

Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ɗazun nan, ta ce taron zai kuma yi nazari kan rikicin siyasar da ke faruwar a ƙasar Senegal sakamakon ɗagen zaɓen shugaban ƙasa da aka tsara gudanarwa a watan nan na Fabrairu. Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka ta ce taron da za ta gudanar a...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:10
ECOWAS na taro kan Nijar, Mali, Burkina Faso da Senegal
Кратко

Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ɗazun nan, ta ce taron zai kuma yi nazari kan rikicin siyasar da ke faruwar a ƙasar Senegal sakamakon ɗagen zaɓen shugaban ƙasa da aka tsara gudanarwa a watan nan na Fabrairu. Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka ta ce taron da za ta gudanar a...

Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ɗazun nan, ta ce taron zai kuma yi nazari kan rikicin siyasar da ke faruwar a ƙasar Senegal sakamakon ɗagen zaɓen shugaban ƙasa da aka tsara gudanarwa a watan nan na Fabrairu. Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka ta ce taron da za ta gudanar a Abuja ranar Alhamis zai mayar da hankali kan fitar ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso daga cikinta. Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ɗazun nan, ta ce taron zai kuma yi nazari kan rikicin siyasar da ke faruwar a ƙasar Senegal sakamakon ɗagen zaɓen shugaban ƙasa da aka tsara gudanarwa a watan nan na Fabrairu. The Extraordinary Session of the MSC will discuss the withdrawal of Niger, Burkina Faso and Mail from the community as well as the political situation in Senegal. — Ecowas - Cedeao (@ecowas_cedeao) February 8, 2024 Ranar 28 ga watan Janairu ne ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso suka sanar da ficewarsu daga ECOWAS sannan suka aika mata da takardar sanarwar fitarsu washegari. “Bayan shekaru 49, jajirtattun al'ummar Burkina Faso da Mali da Nijar cikin nadama tare da nuna rashin jin ɗaɗinsu na ganin cewa (ECOWAS) ta kauce daga aƙidar kakaninmu da suka kafa ta ta kishin Afirka,” kamar yadda Kanal Amadou Abdramane, mai magana da yawun sojojin Nijar, ya bayyana. ECOWAS ta dakatar da ƙasashen uku daga cikinta sannan ta saka musu takunkumai masu tsauri sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi. Hakan ne ya fusata su har ta kai su ga fita daga cikinta, a cewarsu. Doka mai lamba 91 ta ECOWAS ta tanadi cewa dole ne ƙasar da ta bayyana fitarta daga cikin ƙungiyar ta jira tsawon shekara guda kafin ta fita bayar ta bayar da sanarwa a hukumance. Sai dai ranar Laraba Nijar, Mali da Burkina Faso sun sanar cewa nan-take suka fice daga ECOWAS, kuma ba za su yi biyayya ga dokokin ƙungiyar da suka buƙaci su bayar da sanarwar shekara ɗaya kafin su fita daga cikinta ba. 'Dambarwar siyasar Senegal' ECOWAS ta ce rikicin siyasar Senegal na damunta bayan Shugaba Macky Sall sanar da ɗage zaɓen ƙasar wanda aka tsara gudanarwa a ranar 25 ga watan Fabrairun 2024. Ya sanar da hakan a wani jawabi da ya yi wa ƙasar a Dakar babban birnin ƙasar inda ya ce an ɗage zaɓen sakamakon wasu matsaloli da ke tattare da jerin sunayen ƴan takara. A Nuwambar bara ne Mista Sall ya saka ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin ranar zaɓen ƙasar inda ƴan takara 20 za su fafata a zaɓen sai dai a cikin mutanen babu sunayen wasu manyan ƴan adawa. Lamarin ya haifar da zanga-zanga da kuma Allah wadarai daga ciki da wajen ƙasar. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Asabar da maraice, ECOWAS ta bayyana "damuwa game da yanayin da ya sa aka ɗage zaɓukan" sannan ta yi kira ga "hukumomin da suka kamata su yi gaggawar kammala tsare-tsare domin a sanya sabuwar ranar zaɓe."