Dubban mutane sun hallara a Bani Walid domin yi masa bankwana Dubban mutane sun taru a ranar Juma’a a garin Bani Walid da ke arewa maso yammacin Libya domin jana’izar Saif al-Islam Gaddafi, ɗan marigayi shugaban Libya Muammar Gaddafi, wanda aka kashe a farkon wannan makon. TRT Hausa Masu makoki sun ɗauki akwatin gawarsa tare da manyan hotunansa da na mahaifinsa, yayin da aka yi sallar jana’iza kafin a binne shi a garin. Muammar Gaddafi ya yi mulkin Libya sama da shekaru 40 kafin a hambarar da shi a 2011. TRT Hausa Hukumomi sun ce Saif al-Islam, mai shekaru 53, an kashe shi ne ta harbi a gidansa da ke Zintan, inda bincike na farko ya tabbatar da hakan. Ƙungiyarsa ta siyasa ta ce wasu mutane huɗu sanye da abin rufe fuska ne suka kutsa gidan suka kashe shi bayan kashe kyamarorin tsaro. TRT Hausa Ɗan’uwansa Mohamed Gaddafi ya bayyana baƙin cikinsa kan kisan, yana mai cewa ko da yake ba zai iya halartar jana’izar ba, amma ya gamsu da ganin magoya baya sun yi masa bankwana yadda ya dace. TRT Hausa
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
An yi jana’izar Saif al-Islam Gaddafi a Libya
Dubban mutane sun hallara a Bani Walid domin yi masa bankwana Dubban mutane sun taru a ranar Juma’a a garin Bani Walid da ke arewa maso yammacin Libya domin jana’izar Saif al-Islam Gaddafi, ɗan marigayi shugaban Libya Muammar Gaddafi, wanda aka kashe a farkon wannan makon. TRT Hausa Masu makoki s...

At a glance