Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

Dubban mutane ne suka halarci jana'izar Raisi a Tehran

Ali Khamenei, shugaban addini na Iran ne zai jagoranci sallar Jana'iar Raisi da 'yan tawagarsa. Dubban mutane ne suka taru a kan titunan Tehran babban birnin Iran don halartar jana'izar shugaba Ebrahim Raisi da 'yan tawagarsa, waɗanda suka mutu a hatsarin helikkwafta. A ranar Larabar nan a tsakiy...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:10
Dubban mutane ne suka halarci jana'izar Raisi a Tehran
Em resumo

Ali Khamenei, shugaban addini na Iran ne zai jagoranci sallar Jana'iar Raisi da 'yan tawagarsa. Dubban mutane ne suka taru a kan titunan Tehran babban birnin Iran don halartar jana'izar shugaba Ebrahim Raisi da 'yan tawagarsa, waɗanda suka mutu a hatsarin helikkwafta. A ranar Larabar nan a tsakiy...

Ali Khamenei, shugaban addini na Iran ne zai jagoranci sallar Jana'iar Raisi da 'yan tawagarsa. Dubban mutane ne suka taru a kan titunan Tehran babban birnin Iran don halartar jana'izar shugaba Ebrahim Raisi da 'yan tawagarsa, waɗanda suka mutu a hatsarin helikkwafta. A ranar Larabar nan a tsakiyar birnin, mutane sun yi cincirindo ɗauke da hotunan Raisi a jikin alluna a kusa da Jami'ar Tehran, inda Ali Khamenei, shugaban addini na Iran zai jagoranci Sallar Jana'izar Raisi da 'yan tawagarsa da suka haɗa da Ministan Harkokin Waje Hossein Amirabdollahian. A ranar Lahadi ne jirgin helikwafta da Raisi ke ciki ya yi hatsari a wani yanki mai tsaunuka da hazo ya baibaye da ke arewacin Iran a kan hanyarsu ta zuwa Tebriz, bayan halartar ƙaddamar da wata madatsar ruwa a kan iyakar Azerbaijan. Ƙasar Turkiyya na cikin waɗanda suka taimaka wajen gano jirgin da ya faɗi, kamar yadda tashar talabijin ta ƙasar ta bayyana. Ebrahim Raisi: Tarihin shugaban Iran da ya rasu a hatsarin helikwafta Kafin mutuwarsa, ana kallon Raisi, mai shekara 63, a matsayin wanda zai gaji Khamenei a muƙamin shugaban addini na Iran. An aike wa da al'ummar birnin Tehran saƙonni ta wayar salula da ke kira a gare su da su halarci taron Jana'izar. Manyan jami'an ƙasashen waje na halartar taron jana'izar. Za a binne shi a Shahidai A ranar Talata aka fara shirin jana’izar marigayi shugaban ƙasar da ‘yan tawagarsa a garin Tebriz inda dubban mutane sanye da baƙaƙen tufafi suka halarci cibiyar Qom ta babban Malamin Shi'a don yi wa marigayin addu'o'i. Daga Tehran, za a kai gawawwakin zuwa lardin Khorasan ta Kudu, daga nan kuma a kai Raisi garinsu na Mashhad don binne shi a yammacin Alhamis. Khamenei ya ayyana kwanaki biyar na zaman makoki a faɗin ƙasar Iran kuma ya naɗa mataimakin shugaban ƙasa Mohammed Mokhber, mai shekara 68 a matsayin shugaban riƙon ƙwarya.