Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Dubban masu zanga-zanga a Nijar na son dakarun Amurka su bar ƙasar

Ɗalibai da wasu fitattun mutane a gwamnatin mulkin sojin ƙasar suna cikin ɗimbin mutanen da suka hallara a wajen majalisar dokokin ƙasar a Yamai. Dubban masu zanga-zanga a babban birnin Nijar a ranar Asabar sun yi gangamin neman sojojin Amurka su bar kasar nan-take bayan gwamnatin mulkin sojin ka...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:10
Dubban masu zanga-zanga a Nijar na son dakarun Amurka su bar ƙasar
En bref

Ɗalibai da wasu fitattun mutane a gwamnatin mulkin sojin ƙasar suna cikin ɗimbin mutanen da suka hallara a wajen majalisar dokokin ƙasar a Yamai. Dubban masu zanga-zanga a babban birnin Nijar a ranar Asabar sun yi gangamin neman sojojin Amurka su bar kasar nan-take bayan gwamnatin mulkin sojin ka...

Ɗalibai da wasu fitattun mutane a gwamnatin mulkin sojin ƙasar suna cikin ɗimbin mutanen da suka hallara a wajen majalisar dokokin ƙasar a Yamai. Dubban masu zanga-zanga a babban birnin Nijar a ranar Asabar sun yi gangamin neman sojojin Amurka su bar kasar nan-take bayan gwamnatin mulkin sojin kasar ta ce ta janye daga yarjejeniyar soji da Washington. Bayan wani juyin mulkin watan Yuli, kasar ta Yammacin Afirka ta bayyana a tsakiyar watan Maris cewa Amurka ce ta kakaba yarjejeniyar hadin-gwiwar din ta shekarar 2012. Dalibai da kuma wasu fitattun mutane daga cikin gwamnatin mulkin sojin suna cikin gungun mutanen da suka hallara a kofar hedkwatar majalisar dokokin kasar a Yamai. An ji mutanen suna cewa "Tir da mulkin mallakar Amurka" da kuma "Tattakin 'yanta mutane na tafe". Korar Faransa An kori dakarun Faransa a karshen shekarar 2023, amma kimanin sojojin Amurka 1,000 sun ci gaba da kasancewa a birnin Agadez a arewacin kasar. A ƙarshen watan Maris Nijar ta ce Amurka za ta mika wasu shawarwari na "raba" sojojinta da kasar. Washington ta ki cewa komai game da batun, amma ta ce ta tuntubi Nijar domin "samun karin bayani". "Sun ce su(Amurkawan) za su tafi, saboda haka su tafi cikin lumana kuma da wuri ," a cewar Sheikh Ahmadou Mamoudou, wani sanannen malamin addini . Ƙona tutoci An ga mutane riƙe da tutocin ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar da kuma Rasha a yayin gangamin amma waɗanda suka shirya zanga-zangar sun ce a guji maganganun ɓatanci da zagi ga Amurka ko kuma kone tutocinta. A watan Maris Nijar ta haɗa kai da makwabtanta Mali da Burkina Faso wajen kafa wata runduna ta hadin gwiwa domin yakar wadanda suka dade suna ta da kayar baya a ƙasashen uku. Kasashen uku sun juya wa Faransa da ta yi musu mulkin mallaka baya kuma suka karfafa dangantaka da Rasha.