Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

DSS ta gargadi ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya a kan shirin zanga-zangar 'tsadar rayuwa'

Hukumar tsaro ta farin kaya a Nijeriya DSS ta gargaɗin Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasar NLC da ta janye shirin zang-zangar da take yi a ƙasar “don guje wa jawo tashin hankali da hargitsi.” Hukumar tsaro ta farin kaya a Nijeriya DSS ta gargaɗin Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasar NLC da ta janye shirin zang-zangar...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:10
DSS ta gargadi ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya a kan shirin zanga-zangar 'tsadar rayuwa'
De un vistazo

Hukumar tsaro ta farin kaya a Nijeriya DSS ta gargaɗin Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasar NLC da ta janye shirin zang-zangar da take yi a ƙasar “don guje wa jawo tashin hankali da hargitsi.” Hukumar tsaro ta farin kaya a Nijeriya DSS ta gargaɗin Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasar NLC da ta janye shirin zang-zangar...

Hukumar tsaro ta farin kaya a Nijeriya DSS ta gargaɗin Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasar NLC da ta janye shirin zang-zangar da take yi a ƙasar “don guje wa jawo tashin hankali da hargitsi.” Hukumar tsaro ta farin kaya a Nijeriya DSS ta gargaɗin Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasar NLC da ta janye shirin zang-zangar da take yi a ƙasar “don guje wa jawo tashin hankali da hargitsi.” A sanarwar da ta fitar a ranar Laraba, DSS ta ce duk da cewa hukumar ƙungiyar ƙwadago na da damar shirya hakan bisa kundin tsarin mulki, tana ganin “bin tsarin tattaunawa zai fi kamata maimakon yin abin da zai tayar da hankula.” Tun da fari Ƙungiyar Ƙwadago ta sanar da shirya yin zanga-zangar a ranar Alhamis da nufi nuna takaicinsu kan halin matsi da tsadar rayuwa da ake ciki a Nijeriyar. “Hukumar DSS tana sane da cewa wasu ɓata gari suna shirin amfani da zanga-zangar don ƙirƙirar rikici da jawo tashin hankali,” ta faɗa a sanarwar da ta wallafa a shafinta na X. Ta ce a ganinta babu abin da zanga-zangar za ta yi sai ƙara ta’azzara yanayin zamantakewar tattalin arziki da ake ciki a faɗin ƙasar.