Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

DRC ta yanke wa tsohon Shugaba Joseph Kabila hukuncin kisa

Wata kotun sojoji a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ta yanke wa tsohon Shugaban kasar Joseph Kabila hukuncin kisa a bayan idonsa, bisa samunsa da laifuka, ciki har da laifukan yaƙi. Wata kotun soja a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta yanke wa tsohon Shugaban Ƙasar Joseph Kabila hukuncin kisa a b...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:10
DRC ta yanke wa tsohon Shugaba Joseph Kabila hukuncin kisa
Kwa muhtasari

Wata kotun sojoji a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ta yanke wa tsohon Shugaban kasar Joseph Kabila hukuncin kisa a bayan idonsa, bisa samunsa da laifuka, ciki har da laifukan yaƙi. Wata kotun soja a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta yanke wa tsohon Shugaban Ƙasar Joseph Kabila hukuncin kisa a b...

Wata kotun sojoji a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ta yanke wa tsohon Shugaban kasar Joseph Kabila hukuncin kisa a bayan idonsa, bisa samunsa da laifuka, ciki har da laifukan yaƙi. Wata kotun soja a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta yanke wa tsohon Shugaban Ƙasar Joseph Kabila hukuncin kisa a bayan idonsa, sakamakon samunsa da laifuffuka da suka haɗa da laifukan yaƙi. Laftanar Janar Joseph Mutombo Katalayi, wanda ya jagoranci kotun ta soja a babban birnin ƙasar, ya bayyana a ranar Talata cewa, an samu Kabila da laifufuka daban-daban, ciki har da cin amanar ƙasa, da laifukan cin zarafin bil'adama, da kisan kai, da fyade, da azabtarwa, da tayar da ƙayar baya. Kabila ya shafe kusan shekaru ashirin yana mulki kuma ya sauka daga mulki ne kawai bayan mummunar zanga-zangar adawa da gwamnatinsa. Tun daga ƙarshen shekarar 2023, Kabila ya koma Afirka ta Kudu da zama, duk da cewa ya bayyana a Goma, wani yanki da 'yan tawaye ke iko da shi a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, a watan Mayu.