Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Dole mu ɗauki masu satar mutane don kuɗin fansa a matsayin ƴan ta’adda – Shugaba Tinubu

''Dole ne mu ɗauki masu garkuwa da mutane a matsayin 'yan ta'adda. Su matsorata ne. Wulƙantattu ne su. Suna kai hari kan marasa ƙarfi," in ji Shugaba Tinubu. Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Yinubu ya ce daga yanzu duk wasu masu aikata “ƙazamin” laifi irin na satar mutane don karɓar kuɗin fansa za a...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:10
Dole mu ɗauki masu satar mutane don kuɗin fansa a matsayin ƴan ta’adda – Shugaba Tinubu
De un vistazo

''Dole ne mu ɗauki masu garkuwa da mutane a matsayin 'yan ta'adda. Su matsorata ne. Wulƙantattu ne su. Suna kai hari kan marasa ƙarfi," in ji Shugaba Tinubu. Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Yinubu ya ce daga yanzu duk wasu masu aikata “ƙazamin” laifi irin na satar mutane don karɓar kuɗin fansa za a...

''Dole ne mu ɗauki masu garkuwa da mutane a matsayin 'yan ta'adda. Su matsorata ne. Wulƙantattu ne su. Suna kai hari kan marasa ƙarfi," in ji Shugaba Tinubu. Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Yinubu ya ce daga yanzu duk wasu masu aikata “ƙazamin” laifi irin na satar mutane don karɓar kuɗin fansa za a ɗauke su a matsayin ƴan ta’adda. Da yake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na fatattakar ‘yan bindiga, Shugaban Kasar ya ce wadanda ke yin garkuwa da yara matsorata ne, wadanda ba za su iya tinkarar ƙarfin sojojin Nijeriya ba. Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake buɗa-baki da alkalan gwamnatin tarayya a ranarTalata, ƙarƙashin jagorancin Alkalin-Alkalai na Nijeriya Mai Shari’a Olukayode Ariwoola. ''Dole ne mu ɗauki masu garkuwa da mutane a matsayin 'yan ta'adda. Su matsorata ne. Wulƙantattu ne su. Suna kai hari kan marasa ƙarfi. “Suna zuwa makarantu suna sace yara suna haifar da rashin jituwa. Dole ne mu ɗauke su daidai a matsayin 'yan ta'adda don mu kawar da su, kuma na yi muku alkawarin za mu kawar da su,” in ji Shugaban Ƙasar. Waɗannan kalamai na Tinubu na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da hukumomi suka ceto yara ƴan makarantar firamare da aka sace a garin Kuriga na jihar Kaduna mako biyu da suka wuce. Tun da fari a ranar Talatar, Shugaba Tinubu ya gana da gwamnan jihar Zamfara, inda matsalar satar mutane da fashi da makami ta fi ƙamari, kuma gwamnan ya ce Shugaban Ƙasa ya yi alkawarin taimakawa don kawo ƙarshen “bala’in” da jihar ke fama da shi na rashin tsaro. Nijeriya na fama da matsalolin rashin tsaro daban-daban, musamman a jihohin arewa maso yamma irin su Zamfara da Kaduna da Katsina da Neja da Sokoto. Sai dai Tinubu ya sha nanata cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa sasantawa da ƴan bindiga ba ko kuma ba su kuɗin fansa. A hannu guda kuma, Shugaban Ƙasar ya sha alwasin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauye don inganta yanayin aikin ma’aikatan shari'a a ƙasar. Kazalika ya gode musu da nuna jin daɗinsa ga bangaren shari’a bisa sadaukarwar da suke yi wa ƙasa, inda ya yaba da rawar da suke takawa wajen tabbatar da martabar bangaren shari’a na gwamnati.