Fidan da Blinken sun tattauna kan mummunan halin jinƙai a Gaza na Falasɗinu da kuma batun yaƙin Rasha da Ukraine. Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jaddada wa Sakataren Waje na Amurka Antony Blinken buƙatar cewa dole ne a dakatar da kisan ƙare dangin da ake yi a Gaza ba tare da ɓata lokaci ba. Ya jaddada masa hakan ne a wata ganawa da suka yi a birnin Riyadh na Saudiyya a ranar Litinin, inda Fidan ya ce dole a matsa wa Isra'ila lamba don kawo ƙarshen kisan ƙare dangin, ta hanyar tsagaita wuta ta dindindin, da kuma kai kayan agaji Gaza. Fidan da Blinken sun tattauna a kan abin da ke faruwa a Gaza a baya-bayan nan, kamar yadda majiyoyin diflomasiyya suka ce. Sun kuma tattauna kan halin da ake ciki a yanzu a Ukraine da kuma dangantakar diflomasiyyar da ke tsakanin Ankara da Washington. Minister of Foreign Affairs @HakanFidan met with Antony Blinken, US Secretary of State, in Riyadh. ???????????????? pic.twitter.com/FR38BglD8S — Turkish MFA (@MFATurkiye) April 29, 2024 Taron masu ruwa da tsaki a kan Gaza Fidan da Blinken sun yi ƙwarya-ƙwaryar ganawar ne ta masu ruwa da tsaki a lamarin Gaza, a wani ɓangare na Babban Taron Tattalin Arziki na Duniya, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Turkiyyan ya wallafa a shafin X. An samar da ƙungiyar masu ruwa da tsaki kan Gaza ta Gaza Contact Group ne a wani taron Ƙungiyar Ƙasashen Musulmai OIC da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa a watan Nuwamba don dakatar da rikicin da ake yi a Gaza da kuma taimakawa wajen cimma zaman lafiya na dindindin. Isra'ila ta ƙddamar da mummunan yaƙi a kan Falasɗinu tun bayan da ƙungiyar Hamas ta kai mata wani harin ba-zata ranar 7 ga watan Oktoban bara. An kashe Falasɗinawa kusan 34,500 tun lokacin, waɗanda mafi yawansu mata ne da yara, sannan an jikkata fiye da mutum 77,600, tare da lalata gine-gine da abubuwan more rayuwa, lamarin da ya jawo fama da ƙarancin abubuwan buƙata.
Архив новостей
В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.
Dole a dakatar da kisan ƙare dangi ba tare da ɓata lokaci ba a Gaza: Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan
Fidan da Blinken sun tattauna kan mummunan halin jinƙai a Gaza na Falasɗinu da kuma batun yaƙin Rasha da Ukraine. Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jaddada wa Sakataren Waje na Amurka Antony Blinken buƙatar cewa dole ne a dakatar da kisan ƙare dangin da ake yi a Gaza ba tare da ɓata...

Кратко
Fidan da Blinken sun tattauna kan mummunan halin jinƙai a Gaza na Falasɗinu da kuma batun yaƙin Rasha da Ukraine. Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jaddada wa Sakataren Waje na Amurka Antony Blinken buƙatar cewa dole ne a dakatar da kisan ƙare dangin da ake yi a Gaza ba tare da ɓata...
