Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Darajar kudin kirifto na Bitcoin ta zarta dala dubu 40

Farashin kudin kirifto na Bitcoin ya zarta $40,000 a karon farko a yayin da masu zuba hannun-jari suka nuna kwarin gwiwa kan yiwuwar bari a rika harkokin kasuwanci da shi a Amurka. Farashin kowanne kudin kirifto na Bitcoin ya kai $40,000 ranar Litinin din nan a karon farko tun watan Mayun shekara...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:09
Darajar kudin kirifto na Bitcoin ta zarta dala dubu 40
De un vistazo

Farashin kudin kirifto na Bitcoin ya zarta $40,000 a karon farko a yayin da masu zuba hannun-jari suka nuna kwarin gwiwa kan yiwuwar bari a rika harkokin kasuwanci da shi a Amurka. Farashin kowanne kudin kirifto na Bitcoin ya kai $40,000 ranar Litinin din nan a karon farko tun watan Mayun shekara...

Farashin kudin kirifto na Bitcoin ya zarta $40,000 a karon farko a yayin da masu zuba hannun-jari suka nuna kwarin gwiwa kan yiwuwar bari a rika harkokin kasuwanci da shi a Amurka. Farashin kowanne kudin kirifto na Bitcoin ya kai $40,000 ranar Litinin din nan a karon farko tun watan Mayun shekarar da ta gabata, bayan da masu mu'amala da shi suka samu kwarin gwiwa cewa nan ba da jimawa ba Amurka za ta bari a rika amfani da shi wajen harkokin kasuwanci. Darajar kudin na kirifto ta tashi sosai a wannan shekarar, inda ta ninka da kusan kashi 150, bayan da mutane suka samun kwarin gwiwa cewa nan gaba kadan hukumomin da ke sanya ido kan hada-hadar kudi za su bari a soma amfani da shi. Hakan zai sa a rika bibiyar farashin kudin na bitcoin da kuma barin jama'a su sanya hannun-jari a cikinsa kai-tsaye. Kamfanin Ferrari zai soma karbar kirifto domin sayar da motoci "Wannan manufa ta amfani da wannan kudi a kasuwanni hannun-jari... ana sa rai sosai kuma hakan zai daukaka darajar bitcoin," in ji Lucy Guzmararian, mai kamfanin Token Bay Capital, a hirarta da Bloomberg. An sayar da Bitcoin a kan $40,700 da misalin karfe hudu na safe a agogon GMT ranar Litinin.