Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Dangote ya koma matsayinsa na wanda ya fi kowa kudi a Afirka

A halin yanzu arzikin Dangote ya kai dala biliyan 10.5, kamar yadda wani jerin mutanen da suka fi arziki a duniya ya nuna Fitaccen mai kudin nan na Nijeriya Aliko Dangote ya koma matsayinsa na wanda ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, kasa da mako guda bayan mai kudin nan na Afirka ta Kudu Johann R...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:09
Dangote ya koma matsayinsa na wanda ya fi kowa kudi a Afirka
En bref

A halin yanzu arzikin Dangote ya kai dala biliyan 10.5, kamar yadda wani jerin mutanen da suka fi arziki a duniya ya nuna Fitaccen mai kudin nan na Nijeriya Aliko Dangote ya koma matsayinsa na wanda ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, kasa da mako guda bayan mai kudin nan na Afirka ta Kudu Johann R...

A halin yanzu arzikin Dangote ya kai dala biliyan 10.5, kamar yadda wani jerin mutanen da suka fi arziki a duniya ya nuna Fitaccen mai kudin nan na Nijeriya Aliko Dangote ya koma matsayinsa na wanda ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, kasa da mako guda bayan mai kudin nan na Afirka ta Kudu Johann Rupert ya doke shi, kamar yadda mujallar Forbes ta tabbatar. A halin yanzu arzikin Dangote ya kai dala biliyan 10.5, kamar yadda wani jerin mutanen da suka fi arziki a duniya ya nuna. Ya sauka daga matakin tun a farko bayan ya samu raguwa da dala biliyan 3.8. Dangote a baya ya rike kambin wanda ya fi kowa kudi a Afirka na sama da shekara 10. Shi ne mai hannun jari mafi tsoka a kamfanin simintin Dangote. Fitaccen mai arzikin ya bude matatar mai mafi girma a Afirka a watan Mayun 2023 wadda za ta iya tace ganga 650,000 a kullum. Tun daga 1987 Forbes ke bibiyar shahararrun masu biliyoyin kudi na duniya. Ga jerin mutum goma wadanda suka fi kudi a Afirka: Aliko Dangote - Nijeriya, $10.5 billion Johann Rupert da iyalai - Afirka ta Kudu, $10 billion Nicky Oppenheimer da iyalai - Afirka ta Kudu, $8.3 billion Nassef Sawiris - Masar, $7.2 billion Abdulsamad Rabiu - Niijeriya, $6.3 billion Nathan Kirsh - Eswatini, $5.9 billion Issad Rebrab da iyalai - Algeria, $4.6 billion Mohamed Mansour - Masar, $3.6 billion Naguib Sawiris - Masar, $3.3 billion Mike Adenuga - Nijeriya, $3.2 billion