Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Dan sama jannatin Turkiyya na 2 zai bi jirgin Virgin Galactic da zai yi zagaye a sararin samaniya

Tafiyar da ɗan sama jannati Atasever zai yi da jirgin Virgin Galactic na zuwa ne bayan bulaguron ɗan sama jannatin Turkiyya na farko a watan Janairu zuwa Tashar Ƙasa da Ƙasa ta Sararin Samaniya a shirin Axiom Mission 3 mission. Dan sama jannati na biyu na Turkiyya Tuva Cihangir Atasever, zai kasa...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:09
Dan sama jannatin Turkiyya na 2 zai bi jirgin Virgin Galactic da zai yi zagaye a sararin samaniya
At a glance

Tafiyar da ɗan sama jannati Atasever zai yi da jirgin Virgin Galactic na zuwa ne bayan bulaguron ɗan sama jannatin Turkiyya na farko a watan Janairu zuwa Tashar Ƙasa da Ƙasa ta Sararin Samaniya a shirin Axiom Mission 3 mission. Dan sama jannati na biyu na Turkiyya Tuva Cihangir Atasever, zai kasa...

Tafiyar da ɗan sama jannati Atasever zai yi da jirgin Virgin Galactic na zuwa ne bayan bulaguron ɗan sama jannatin Turkiyya na farko a watan Janairu zuwa Tashar Ƙasa da Ƙasa ta Sararin Samaniya a shirin Axiom Mission 3 mission. Dan sama jannati na biyu na Turkiyya Tuva Cihangir Atasever, zai kasance a cikin jirgin bincike na VSS Unity na kamfanin Virgin Galactic da zai zagaye sararin duniya a ranar Asabar, wanda zai tashi daga jihar New Mexico ta Amurka, a bulaguro na ƙarsh da jirgin zai yi. Jirgin na VSS Unity yana ɗauke da matuƙa biyu, sannan yana da na'urorin da za su ba shi damar sauka a duniyarmu ta Earth bayan harab shi sararin samaniya, inda gudunsa zai wuce na ƙara sau uku a cikin minti ɗaya, da kuma nisan fiye da kilomita 15 daga sararin duniya. An fara harba jirgin sararin samaniya ne a watan Disamban 2018, sai kuma a watan Yulin 2021 ya fara tafiya da mutane, kafin daga bisani a mayar da shi jirgin ɗaukar fasinja a watan Yulin 2023. Atasever zai kasance a cikin jirgin a bulaguron jirgin na ƙarshe. A watan Mayu ne Kamfanin Virgin Galactic ya sanar da cewa ya buɗe sabuwar tasha a Kudancin California don samar da sabon samfurin jirgin sama jannati na Delta, wanda zai iya zagaye sau takwas a sararin saaniya cikin wata ɗaya. Tafiyar da ɗan sama jannati Atasever zai yi da jirgin Virgin Galactic na zuwa ne bayan bulaguron ɗan sama jannatin Turkiyya na farko a watan Janairu zuwa Tashar Ƙasa da Ƙasa ta Sararin Samaniya a shirin Axiom Mission 3 mission.