Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Dan Afirka ta Kudu ya maye gurbin Dangote a matsayin wanda ya fi kudi a Afirka

Sai dai kuma har yanzu dai Dangote ne ke kan gaba a cikin jerin attajirai da suka fi kudi a Afirka a jerin attajirai na jaridar Bloomberg da kudi dala biliyan $15.4bn yayin da Johann Rupert ke biye da shi da kudi dala biliyan $12bn. Dan Afirka ta Kudu, Johann Rupert, ya sha gaban attajirin Nijeri...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:09
Dan Afirka ta Kudu ya maye gurbin Dangote a matsayin wanda ya fi kudi a Afirka
A taƙaice

Sai dai kuma har yanzu dai Dangote ne ke kan gaba a cikin jerin attajirai da suka fi kudi a Afirka a jerin attajirai na jaridar Bloomberg da kudi dala biliyan $15.4bn yayin da Johann Rupert ke biye da shi da kudi dala biliyan $12bn. Dan Afirka ta Kudu, Johann Rupert, ya sha gaban attajirin Nijeri...

Sai dai kuma har yanzu dai Dangote ne ke kan gaba a cikin jerin attajirai da suka fi kudi a Afirka a jerin attajirai na jaridar Bloomberg da kudi dala biliyan $15.4bn yayin da Johann Rupert ke biye da shi da kudi dala biliyan $12bn. Dan Afirka ta Kudu, Johann Rupert, ya sha gaban attajirin Nijeriya, Aliko Dangote, a matsayin wanda ya fi kudi a nahiyar Afirka. Sabon jerin attajiran da suka fi arziki a duniya da mujallar Forbes ta fitar ya nuna cewa Dangote ya sauko daga matsayin ne bayan dala biliyan $3.8bn ya ragu daga cikin arzikinsa. Mujallar ta ce arzikin Dangote ya koma dala biliyan $9.7 a watan Janairun shekarar 2024., yayin da arzikin Johann Rupert dan kasar Afirka ta Kudu ya koma dala biliyan 10 a cikin watan Janairun shekarar 2024. Duk da cewar shi ma attajirin Afirka ta Kudun ya rasa dala miliyan $700m cikin arzikin nasa, shi ne ya fi arziki a nahiyar Afirka, in ji mujallar ta Forbes. Johann Rupert mai shekara 73 dai shi ne shugaban kamfanin kayan alatu na Compagnie Fiannciere Richemonte da ke kasar Switzerland. Johann Rupert ne ya maye gurbin Aliko Dangote a matsayin attajirin da ya fi kudi a Afirka a mujallar Forbes:Hoto/Reuters Sai dai kuma har yanzu dai Dangote ne yake kan gaba a cikin jerin attaijirai da suka fi kudi a Afirka a jerin attajirai na jaridar Bloomberg da kudi dala biliyan $15.4bn yayin da Johann Rupert ke biye da shi da kudi dala biliyan $12bn. Kazalika Abdulsamad Rabiu, shugaban kamfanin BUA, ya koma attajiri na shida da ya fi kudi a Afirka daga matsayi na hudu da yake kai a baya, in ji mujallar Forbes. Shi kuma Mike Adenuga, shugaban kamfanin Globacom, ya koma na 10 daga matsayi na shida a jerin attajiran da suka fi kudi a Afirka, a cewar Forbes. Ana ganin karyawar darajar kudin Naira ta Nijeriya da darajar kudin Rand na Afirka ta Kudu ya taka rawa wajen rage yawan arzikin attajiran na Afirka a rahoton mujallar Forbes.