Ana ta ce-ce-ku-ce tun bayan da aka ga wata takarda dauke da sa hannun ministar ayyukan jinkai inda ta bayar da umarnin biyan kudin rage radadin talauci har sama da miliyan 500 a asusun bankin mutum guda. Akanta Janar ta Nijeriya Dakta Oluwatoyin Madein ta yi karin haske kan cewa ofishinta ba ya biyan kudi a madadin ma’aikatu da hukumomin gwamnati kan ayyukan da suke aiwatarwa. Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar inda take mayar da martani dangane da wasu rahotanni da ake yadawa a shafukan sada zumunta inda ma’aikatar ayyukan jin kai ke neman a biya kudin tallafi ga wasu ‘yan kasar da ke cikin talauci. A bayanin da ta yi, ta ce kowace hukuma ana ware mata kasonta a cikin kasafin kudi kuma kowace hukuma ita ke da hakkin aiwatar da wadannan ayyuka da kuma biyan kudin ayyukan. Tun bayan da aka ga wata takarda dauke da sa hannun ministar ayyukan jin kai ta Nijeriya inda ta bayar da umarnin biyan kudin rage radadin talauci har sama da miliyan 500 a asusun bankin mutum guda ake ta ce-ce-ku-ce. Dakta Oluwatoyin ta ce duk da cewa ofishinta ya samu bukatar biyan wadannan kudade daga ma’aikatar, amma bai biya ba. Ta bayyana cewa sai dai ta bayar da shawara ga ma’aikatar kan irin matakan da ya kamata ta dauka domin ganin an biya wadannan kudaden. Akanta Janar din ta bayyana a irin wadannan lamura, ma’aikatun da abin ya shafa ne ke biyan kudin, kuma babu wasu makudan kudade da za a iya biya ga asusun wani mutum daya da sunan Akanta mai gudanar da ayyuka. A cewarta, ya kamata a tura wa wadanda za su yi amfani da tallafin kowa a asusun bankinsa.
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Dalilin da ya sa na yi watsi da bukatar Ministar Jinkai Betta Edu: Akanta Janar ta Nijeriya
Ana ta ce-ce-ku-ce tun bayan da aka ga wata takarda dauke da sa hannun ministar ayyukan jinkai inda ta bayar da umarnin biyan kudin rage radadin talauci har sama da miliyan 500 a asusun bankin mutum guda. Akanta Janar ta Nijeriya Dakta Oluwatoyin Madein ta yi karin haske kan cewa ofishinta ba ya...

Ana ta ce-ce-ku-ce tun bayan da aka ga wata takarda dauke da sa hannun ministar ayyukan jinkai inda ta bayar da umarnin biyan kudin rage radadin talauci har sama da miliyan 500 a asusun bankin mutum guda. Akanta Janar ta Nijeriya Dakta Oluwatoyin Madein ta yi karin haske kan cewa ofishinta ba ya...
