Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Congo DR da Zambia sun fara tattaunawa game da rufe kan iyaka

Ƙasashen Jumhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo da Zambia sun fara tattaunawa bayan Zambian ta rufe iyakarsu, batun da ya janyo rikici ga Congo, kasa ta biyu a duniya wajen fitar da ƙarfe Copper. Jumhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo ta ce ta fara tattaunawa da Zambia kwana guda bayan da maƙociyarta ta kudanc...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:09
Congo DR da Zambia sun fara tattaunawa game da rufe kan iyaka
Bu haberde ne var?

Ƙasashen Jumhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo da Zambia sun fara tattaunawa bayan Zambian ta rufe iyakarsu, batun da ya janyo rikici ga Congo, kasa ta biyu a duniya wajen fitar da ƙarfe Copper. Jumhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo ta ce ta fara tattaunawa da Zambia kwana guda bayan da maƙociyarta ta kudanc...

Ƙasashen Jumhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo da Zambia sun fara tattaunawa bayan Zambian ta rufe iyakarsu, batun da ya janyo rikici ga Congo, kasa ta biyu a duniya wajen fitar da ƙarfe Copper. Jumhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo ta ce ta fara tattaunawa da Zambia kwana guda bayan da maƙociyarta ta kudancin Afirka ta rufe iyakarsu. Matakin ya toshe babbar hanyar da Congo ke amfani da ita don fitar da Copper zuwa ƙasashen waje, a matsayinta na ƙasa ta biyu a duniya a yawan fitar da ƙarfen Copper. A ranar Asabar, ministan Kasuwanci na Zambia, Chipoka Mulenga ya sanar da rufe iyakar na wani ɗan lokaci, bayan haramcin amfani da wai lemon zaki da barasa a Congo ta yi ya janyi zanga-zangar direbobin dakon kaya a garin Kasumbalesa da ke iyakar Zambia. "An fara tattaunawa tsakanin gwamnatocin Congo da Zambia tun ranar Lahadin nan don hanzarta sake bude kofar iyakar tasu," in ji wata sanarwa da Ma'aikatar Kasuwanci ta Congo ta fitar a ranar Lahadi. "A awannin da suka biyo baya, bangarorin biyu za su hadu a Lubumbashi da ke Haut-Katanga don nemo mafita ta karshe game da kasuwancin." Sanarwa a hukumance Ministan Kasuwanci na Congo Julien Paluku Kahongya ya fitar da sanarwa a ranar Lahadi inda yake cewa ma'aikatarsa ta samu sanarwa a hukumance game da takaddamar kasuwanci daga Zambia kafin ta sanar da rufe iyakar. A sanarwar, ya yi dogon bayani game da yarjejeniyar kasuwancin kasashen biyu da kuma hanyoyin magance duk wata takaddama da ta taso. "Ya zuwa yanzu babu wata takaddama da aka gabatarwa ma'aikatar a rubuce ko ta hanyar diplomasiyya," in shi. "Ma'aikatar ta shirya duba duk wata bukata da Zambia ta kawo matukar tana kunshe a cikin yarjejeniyar, wadda ta hana ramuwar gayya." Congo ce kasa ta biyu a duniya wajen samar da sinadarin Copper, kuma ta zo ta 3 a 2023 wajen fitar da shi, bayan ta fitar da tan miliyan 2.84. Zambia hanya ce mai muhimmanci ga Congo wajen futar da Copper inda ake bi ta garin Kasumbalesa a shigar Zambia.