Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

China Ta Soke Harajin Kayayyaki ga Ƙasashen Afirka

Matakin zai fara aiki daga 1 ga Mayu, banda Eswatini kaɗai Shugaban ƙasar China, Xi Jinping , ya sanar cewa daga 1 ga watan Mayu za a soke duk wani harajin fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen duniya, inda ƙasashen Afirka za su amfana gaba ɗaya, sai dai ƙasa ɗaya kaɗai. TRT Hausa China ta riga ta sok...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:09
China Ta Soke Harajin Kayayyaki ga Ƙasashen Afirka
Em resumo

Matakin zai fara aiki daga 1 ga Mayu, banda Eswatini kaɗai Shugaban ƙasar China, Xi Jinping , ya sanar cewa daga 1 ga watan Mayu za a soke duk wani harajin fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen duniya, inda ƙasashen Afirka za su amfana gaba ɗaya, sai dai ƙasa ɗaya kaɗai. TRT Hausa China ta riga ta sok...

Matakin zai fara aiki daga 1 ga Mayu, banda Eswatini kaɗai Shugaban ƙasar China, Xi Jinping , ya sanar cewa daga 1 ga watan Mayu za a soke duk wani harajin fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen duniya, inda ƙasashen Afirka za su amfana gaba ɗaya, sai dai ƙasa ɗaya kaɗai. TRT Hausa China ta riga ta soke haraji ga ƙasashen Afirka 33, sannan a bara ta bayyana aniyar faɗaɗa tsarin zuwa ƙasashe 53 na nahiyar, a wani mataki na ƙarfafa dangantakar kasuwanci da Afirka. TRT Hausa Daga 1 ga Mayu, duk ƙasashen Afirka ba za su ƙara biyan harajin kwastam ba, sai Eswatini , wadda ke ci gaba da alaƙar diflomasiyya da Taiwan . TRT Hausa China na ikirarin Taiwan a matsayin ɓangare na ƙasarta, inda ta ce akwai yiwuwar amfani da ƙarfi domin ƙwace iko da tsibirin idan buƙata ta taso. TRT Hausa China ita ce babbar abokiyar kasuwanci ta Afirka, tare da manyan ayyukan ababen more rayuwa a nahiyar ta hanyar shirin “Belt and Road”. TRT Hausa Matakin ya zo ne yayin da ƙasashen Afirka ke sake duba alaƙar kasuwanci da China da sauran ƙasashe, bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙaƙaba manyan haraji a duniya a bara. TRT Hausa Xi Jinping ya ce yarjejeniyar za ta buɗe sabbin damammaki ga ci gaban Afirka, inda ya sanar da ranar fara aiwatarwa a lokacin taron shugabannin Afirka na African Union da ke gudana a Ethiopia . TRT Hausa