Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

China ta harba sabon kumbon da ya kai tauraron ɗan'adam mai sansano nesa zuwa samaniya

Wannan shi ne karo na 17 a shekarar 2024 da China ta harba tauraron ɗan'adam, ƙarƙashin shirinta na ci gaban fasahar sararin samaniya. China ta ce ta harba kumbon Long March 2D mai ɗaukar kaya, wanda ya kai tauraron ɗan'adam mai fasahar sansano nesa zuwa sararin samaniya. An harba kumbon da ƙarfe...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:09
China ta harba sabon kumbon da ya kai tauraron ɗan'adam mai sansano nesa zuwa samaniya
At a glance

Wannan shi ne karo na 17 a shekarar 2024 da China ta harba tauraron ɗan'adam, ƙarƙashin shirinta na ci gaban fasahar sararin samaniya. China ta ce ta harba kumbon Long March 2D mai ɗaukar kaya, wanda ya kai tauraron ɗan'adam mai fasahar sansano nesa zuwa sararin samaniya. An harba kumbon da ƙarfe...

Wannan shi ne karo na 17 a shekarar 2024 da China ta harba tauraron ɗan'adam, ƙarƙashin shirinta na ci gaban fasahar sararin samaniya. China ta ce ta harba kumbon Long March 2D mai ɗaukar kaya, wanda ya kai tauraron ɗan'adam mai fasahar sansano nesa zuwa sararin samaniya. An harba kumbon da ƙarfe 7:45 na safe (agogon Beijing) daga cibiyar Ƙaddamar da Kumbo ta Xichang, wadda ke gundumar Sichuan da ke kudu maso yammacin ƙasar. Kumbon ya aika da tauraron ɗan'adam mai suna Yaogan-42 02 zuwa samaniya, a cewar kamfanin dillancin labarai na Xinhua News wanda ke mallakin gwamnati, ranar Lahadi. Wannan shi ne karo na 17 a shekarar 2024, kuma karo na 517 na harba kumbo ajin Long March, wanda shi ne ƙasar take yawan amfani da shi cikin jerin kumbunanta. Kumbon samfurin The Long March 2D, yana amfani da makamashi na ruwa ne, kuma yana da ƙarfin ɗagawa da ya kai tan 300. Yana iya safarar kumbon da ke da nauyin tan-1.3 zuwa samaniya da ɗagawar kilomita 700.