Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

CBN zai sayar da dala ga 'yan canji kan Naira I,590

“Wannan sanarwa ce ga 'yan kasuwar canji (BDCs) da kuma sauran jama'a cewa CBN zai samar da ƙarin kuɗaɗe a wannan ɓangaren na kasuwar canjin kuɗaɗen waje,'' a cewar sanarwar CBN. Babban Bankin Nijeriyya, CBN ya amince ya sayar da ƙudin dala ga 'yan canji don biyan buƙatun kasuwar hada-hadar kudi...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:09
CBN zai sayar da dala ga 'yan canji kan Naira I,590
Kwa muhtasari

“Wannan sanarwa ce ga 'yan kasuwar canji (BDCs) da kuma sauran jama'a cewa CBN zai samar da ƙarin kuɗaɗe a wannan ɓangaren na kasuwar canjin kuɗaɗen waje,'' a cewar sanarwar CBN. Babban Bankin Nijeriyya, CBN ya amince ya sayar da ƙudin dala ga 'yan canji don biyan buƙatun kasuwar hada-hadar kudi...

“Wannan sanarwa ce ga 'yan kasuwar canji (BDCs) da kuma sauran jama'a cewa CBN zai samar da ƙarin kuɗaɗe a wannan ɓangaren na kasuwar canjin kuɗaɗen waje,'' a cewar sanarwar CBN. Babban Bankin Nijeriyya, CBN ya amince ya sayar da ƙudin dala ga 'yan canji don biyan buƙatun kasuwar hada-hadar kudi na bayan fage. CBN ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X mai ɗauke da sa hannun Dakta W.J Kanga babban Darakta a sashin Kasuwanci da hada-hadar kudade na CBN. Sanarwar takardar mai ɗauke da kwanan watan Satumba 25 ta bayyana cewa, CBN ya amince ya sayar da dala dubu 20 ga kowane ɗan canji akan farashin Naira I,590. Sales of Foreign Exchange to BDCs to meet Retail Market Demand for Eligible Invisible Transactions... https://t.co/kBOhjRtX0p pic.twitter.com/XoOWs837T2 — Central Bank of Nigeria (@cenbank) September 26, 2024 “Wannan sanarwa ce ga 'yan kasuwar canji (BDCs) da kuma sauran jama'a cewa CBN zai samar da ƙarin kuɗaɗe a wannan ɓangaren na kasuwar canjin kuɗaɗen waje,'' a cewar sanarwar Babban Bankin. ''Don haka, CBN ya amince ya sayar da dala dubu 20 ga kowane ɗan kasuwar canji akan farashin Naira 1,590, don biyan buƙatun hada-hadar kasuwa,'' in ji CBN. Yana mai ƙari da cewa, CBN ya baiwa dukkan 'yan canji na BDCs damar sayar da dala ga abokan cinikayyarsu kan farashin ribar da bai wuce kaso ɗaya cikin 100 ba bisa ga yadda CBN ya sayar musu. ''Yan canjin kasuwar da suka cika sharuɗɗan CBN, suna iya biyan Naira a cikin asusun aijiya da babban bankin ya basu.'' Kazalika, an mika shaidar saka kuɗi da kuma dukkan wasu takardu da ake buƙata don samun ƙudin CBN a sassan babban bankin a Nijeriya - (Abuja, Awka- Kano da kuma Lagos) don samun damar karbar dala dubu 20,000.