CBN ya ce ya dauki matakin ne saboda bankunan Union da Keystone da Polaris da kwamitocin gudanawarsu sun karya dokoki daban-daban ciki har da cusa kai a ayyukan da suke barazana ga harkokin kudi. Babban Bankin Najeriya CBN ya rusa kwamitocin gudanarwar Bankin Union da Keystone da Polaris. CBN ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Laraba, yana mai cewa ‘’wannan mataki ya zama dole saboda wadannan bankuna da kwamitocin gudanawarsu sun ki bin ka’idoji da tanadin dokar sashe na 12 (c) da (f) da (g)da ( h) na shekarar 2020 kan bankuna da cibiyoyin kudi.’’ ''Laifukan da bankuna suka aikata sun hada da rashin bin ka'idar aiki da gaza gudanar da ayyukan da suka shafi shugabanci da yin watsi da ka'idojin da aka bi wajen ba su lasisi da kuma cusa kai cikin ayyukan da suka haifar da barazana ga harkokin kudi da dai sauransu,'' in ji sanarwar. Press Release: CBN Dissolves the Board and Management of Union Bank, Keystone Bank and Polaris Bank pic.twitter.com/HJmPs8bESD — Central Bank of Nigeria (@cenbank) January 10, 2024 Nada sabbin shugabanni Tuni dai CBN ya fitar da sanarwar nada sabbin shugabannin kwamitocin gudanarwar da za su sa ido tare da gudanar da harkokin da suka shafi bankunan guda uku wato Union da Keystone da kuma Polaris. CBN na so bankuna su karbi adireshin soshiyal midiya na kwastamomi An nada Yetunde Oni a matsayin babban daraktar Bankin Union da kuma Mannir Ubali Ringim a matsayin daraktar gudanarwa, sai kuma Hassan Imam a matsayin babban daraktan Bankin Keystone da kuma Chioma A. Mang a matsayin daraktar gudanarwa. Kazalika an nada Lawal Mudathir Omokayode Akintola a matsayin babban daraktan Bankin Polaris da kuma Chris Oyeka Ofikulu a matsayin daraktan gudanarwa. Sanarwar ta bukaci sabbin shugabannin su kama aiki nan-take. CBN ya jaddada samar da tsaro da kare kudaden masu ajiya da kuma ci gaba da jajircewa wajen cika aikinsa na tabbatar da ingantaccen tsarin hada-hadar kudi a Nijeriya. ''Tsarin Bankinmu ya kasance mai karfi da jariya,'' in ji sanarwar CBN.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
CBN ya rusa kwamitocin gudanarwar wasu bankuna a Nijeriya
CBN ya ce ya dauki matakin ne saboda bankunan Union da Keystone da Polaris da kwamitocin gudanawarsu sun karya dokoki daban-daban ciki har da cusa kai a ayyukan da suke barazana ga harkokin kudi. Babban Bankin Najeriya CBN ya rusa kwamitocin gudanarwar Bankin Union da Keystone da Polaris. CBN ya...

At a glance
CBN ya ce ya dauki matakin ne saboda bankunan Union da Keystone da Polaris da kwamitocin gudanawarsu sun karya dokoki daban-daban ciki har da cusa kai a ayyukan da suke barazana ga harkokin kudi. Babban Bankin Najeriya CBN ya rusa kwamitocin gudanarwar Bankin Union da Keystone da Polaris. CBN ya...
