Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

CBN ya koma sayar da dala ga 'yan canji kan N1,450

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya amince ya sayar da kowace dala ɗaya kan Naira 1,450 ga 'yan kasuwar canji da suka cancanta don samun daidaito da kuma biyan buƙatun kasuwancinsu. Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya koma sayar da dala ga 'yan kasuwar canji da suka cancanta daga ranar Alhamis. Matakin C...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:09
CBN ya koma sayar da dala ga 'yan canji kan N1,450
Em resumo

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya amince ya sayar da kowace dala ɗaya kan Naira 1,450 ga 'yan kasuwar canji da suka cancanta don samun daidaito da kuma biyan buƙatun kasuwancinsu. Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya koma sayar da dala ga 'yan kasuwar canji da suka cancanta daga ranar Alhamis. Matakin C...

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya amince ya sayar da kowace dala ɗaya kan Naira 1,450 ga 'yan kasuwar canji da suka cancanta don samun daidaito da kuma biyan buƙatun kasuwancinsu. Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya koma sayar da dala ga 'yan kasuwar canji da suka cancanta daga ranar Alhamis. Matakin CBN na zuwa ne a daidai lokacin da farashin naira ya sake faɗuwa zuwa 1,570 a kasuwar bayan-fage. A yanzu haka, CBN ya koma sayar wa 'yan kasuwar canji kowace dala a kan Naira 1,450, kamar yadda sanarwar da ke ɗauke da sa hannun muƙaddashin daraktan sashen kasuwanci da musayar kuɗi na CBN, AA Mahdi ta bayyana. ''Sakamakon sauye-sauyen da ake koƙarin samu a kasuwar canji da nufin samun daidaito a farashin canjin Naira, Babban Bankin Nijeriya ya lura da yadda ake ci gaba da samun rashin tabbas a kasuwar,'' in ji sanarwar CBN. Yana ƙara da cewa ''hakan ya yi tasiri wajen ƙara ciyar da kasuwar canjin gaba tare da ƙara hauhawar farashin musayar kuɗin.'' Sales of Foreign Exchange to BDCs to Meet Retail Market Demand for Eligible Invisible Transactions. Kindly click on the provided link to read more - https://t.co/okt99Kk99S pic.twitter.com/JHXRgblqqR — Central Bank of Nigeria (@cenbank) July 18, 2024 "Don haka, CBN ya amince ya sayar da dala ga 'yan kasuwar canji da suka cancanta don samun daidaito da kuma biyan buƙatun kasuwancinsu,'' in ji CBN . Kazalika CBN ya ce ''za a sayar da dala 20,000 ga kowane ɗan kasuwar canji a kan N1,450. Babban Bankin ya kuma gargaɗi 'yan kasuwar canjin da kar su ƙara ribar da ta wuce kashi 1.5 cikin 100 kan kowace dala da suka saya daga CBN ga masu hulɗa da su. Dala, wacce aka sayar da ita a kan Naira 1670 a makon da ya gabata, ta farfaɗo zuwa 1,570 a kasuwar canji, inda a ranar Laraba aka rufe kasuwar a kan farashin Naira 1,565 kan kowace dala.