Kiyaye haddura hakki ne da ya rataya kan masu amfani da tituna, da masu kula da titi, da masu ginawa da kula da tsarin hanyoyi, da kuma masu samar da agaji bayan hadari. Daga Gift Dumedah Shekarar 2024 ta zo kuma buri na farko da ya kamata Afirka ta sa a gaba shi ne dakatar da yawan mace-mace da raunuka a kan hanyoyinmu, ta hanyar sabunta kudurin ''Vision Zero'' da kuma habaka tsarin aminci a Afirka. Vision Zero wani tsarin dabaru ne na kawo karshen asarar rayuka da munanan raunuka da ake samu a kan tituna, tare da tabbatar da lafiya da ingancin tsarin sufuri ga kowa. Habaka wannan tsarin a Afirka na nufin ceto rayukan mutane kusan 27 a cikin duk mutune 100,000, sannan da kusan kashi 7 cikin 100 na dukiya a ma'unin GDP na tattalin arzikin kasashe a nahiyar cikin shekara guda. Wannan kididdigar ba ta hada da mummunan tasirin zamantakewa da kuma lafiyar kwakwalwar mutane, da kuma iyalai ke fuskanta ba, sakamakon hadurran da ake samu a hanyoyi. Daga watan Janairu zuwa Oktoban shekarar 2023, an fitar da rahoton mutuwar mutane 3,609 a Kenya, sannan a Ghana an samu asarar rayuka 1,839 da kuma wadanda suka jikkata mutum12,678. A cewar cibiyar Bankin Duniya, kasashe irinsu Nijeriya da Habasha da Afirka ta kudu da kuma Sudan, su ne suke daukar adadin rabin mace-macen da ake samu sakamakon hadurra a kan hanyoyi a yankin kudu da hamadar Sahara. Nijeriya ce ta fi kowacce kasa yawan mace-macen mutane sakamakon hadurran ababen hawa a duniya, da kusan mutane 52.4 cikin mutane 100,000, sai kuma kasar Mozambique da ke biye mata a matsayi na biyu a nahiyar Afirka, da kusan mutane 46.7 cikin mutum 100,000. Hakkin da ya rataya a kan kowa An gano cewa dabarun Vision Zero na sadaukar da kai ne kan dakile mace-mace da kuma munanan raunuka a tsarin hanyoyimmu. Akwai yiwuwar cimma hakan saboda za a iya kawo karshen hadurran ababen hawa. Hanyoyi marasa kyau na daga cikin abubuwan da ke haddasa hadurra a Afirka. / Hoto: Getty A cewar rahoton shekarar 2023 na Hukumar Lafiya ta duniya, WHO, kan kiyaye haddura a hanyoyi, yawan mace-mace sanadin hadarin ababen hawa a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2021, na raguwa a kowace nahiya, ban da nahiyar Afirka da aka samu karin kashi 17 cikin 100, duk da karancin ababen hawa da kuma karancin manyan hanyoyin motoci da ake da su. Sannan an gano cewa mafi yawan motocin da ake da su a Afirka ba su da inganci, saboda siyasar tattalin arziki da ake yi wajen shigo da motoci zuwa yankin, wanda a karshe ba sa cika ka'idojin kiyayewa da na muhalli. Rahoton ya yi nuni da cewa mace-macen da ake samu a sanadiyar hadurra kan hanyoyi a duniya na raguwa. Haka nan, kasashen da suka rungumi tsarin kiyayewa na kula da ka'idojin hanya su suka fi cin riba. Dabarun kiyayewar na jaddada cewa, kiyaye haddura hakki ne da ya rataya kan masu amfani da tituna, da masu kula da titi, da masu ginawa da kula da tsarin hanyoyi, da kuma masu samar da agaji bayan hadari. Tsarin na amfani da muhimman ka'idoji biyar wadanda ke jaddada cewa, ba a amince a samu rauni ko a mutu ba. Mutane suna yin kuskure, mutane suna da rauni, ba za a yi kasa a gwiwa ba kan kiyayewa, sannan samar da wasu hanyoyi yana da muhimmaci wajen kafa matakan tsaro. Idan aka mai da hankali kan wadannan ka'idoji da abubuwa da aka lissafo, tsarin kiyayewar zai samar da yanayin hanya mai kyau, tare da rage yawan hadurran ababen hawa da kuma mace-mace da raunuka da ake samu. Kuskuren dan'adam Baya ga hangen nesa a tsarin na musamman, shirin ya kuma fita daban saboda abubuwan da ya kunsa. Shirin ya dogara ne kan 'dan adam, wajen mai da hankali kan tsaron masu amfani ta hanyar kawo wasu canje-canje ga yanayin amfani, da ababen hawa da kuma tsarin gina manyan hanyoyi. Tsarin kiyayewar na amfani na'urar da ke hangen nesa da kuma yin duba kan tsare-tsare da yanayin jikin mutum, gami da gina hanyoyi da ababeb hawa da kuma kula da gudun ababen hawa. Hanyar tana amfani da tsarin kaucewa kuskuren dan' adam, ta inda ake jaddada bukatar tsara tsarin sufuri da aikinsa, don rage cutarwa, tare da yarda kan cewa masu amfani da hanya suna iya yin kuskure, sannan a wani lokacin suna iya yanke shawara mara kyau. Wato jikin dan'adam yana da yanayin da zai iya jure hadurran ababen hawa a hanya, kafin ya kai ga mutuwa ko wani mummunan rauni. Mutuwar da ta fi cuta A matsayin wani tsari mai fa'ida, tsarin tsaron yana aiki ta hanyar magance matsalolin kiyayewa da suka shafi ababen more rayuwa, da halayen 'dan adam da kuma sanya ido kan duk wani abin hawa, da masana'antar sufuri, da kuma hanyoyin kai daukin gaggawa. Wani hadarin motar bas a Afirka ta Kudu. / Hoto: Wasu Duk da an tabbatar da ingancin wannan tsari da kuma karbuwa da tasirinsa a fadin duniya, me ya sa har yanzu aiwatar da shi ya zama jan aiki ga kasashen Afirka da dama? A zahiri dai, akwai wasu sauye-sauye da kalubale da ke gaba, wadanda ke hana kasashen Afirka daukar dabarun tsarin kiyaye haddura. Batun da ke kan gaba a cikin su shi ne, ba a cika ba da fifiko kan samar da aminci a kan hanyoyi ba. Ba a dauki hakan a matsayin wata babbar matsala ba. Alamu sun yi nuni da hakan a kasafin kudin da ake ware wa bangaren don inganta kariyar hanyoyin da kuma takaita samun raunuka. Ga misali, Shirin Ayyukan Kare Hadurra na Afirka yana karfafa gwiwar kasashen Afirka da su ware akalla kashi 10 cikin 100 na jarin ababen more rayuwasu, ga samar da kyawawan hanyoyi. Duk da cewa yana da wuya a iya tabbatar da ainihin kasafin kudin kasa, amma akwai kalubalen da suka shafi rashin wadatattun albarkatu da abubuwan da aka fi mai da hankali a kansu da kuma ra'ayi na siyasa. Raunukan da ake samu sanadin hadurran ababen hawa na daga cikin manyan dalilan da ke janyo mutuwa a nahiyar Afirka, baya ga zazzabin cizon sauro da tarin fuka, a cewar rahotannin WHO da dama. Duk da haka, bangaren ba ya samun isasshen jari da tallafin kudi da ingantattun ababen more rayuwa, ko kuma isassun ayyukan bincike da ci gaba. Ba a aiki a zahirance Kenya na daga cikin kasashen da ke fama da mafi munin hadurran motoci a nahiyar Afirka. / Hoto: TRT Afrika Sai dai ana iya cewa, akwai tarin damammaki a shekarar 2024 da za a samu ci gaban bangaren kiyaye haddura, da kuma takaita raunuka ta hanyar amfani da dabarun tsarin kiyayewa a Afirka. A yanzu haka ana kan gine-gine hanyoyin sufuri da ababen more rayuwa a Afirka, da kuma fatan za a samar da matakan aminci masu inganci kai-tsaye. Amma dukkan wadannan ba za su samu kai tsaye ba, idan ba a yi tsayin daka da kokarin hadin kan kowane bangare ba. Dole a ba da fifiko ga rayukan 'dan adam a kan hanyoyinmu. Za a iya cimma kudurin tsarin Vision zero na ceton rayuka a kan titunanmu ta hanyar bin dabarun tsarin kiyayewa. Don cimma kudurin guda, sai masu ruwa da tsaki sun sauke nauyin da ya rataya a wuyansu wajen tabbatar da cewa an aiwatar da dukkan ayyukan da aka sa a gaba, da suka shafi na'urori da tsare-tsare, da yanayin muhallin 'dan adam ciki har da tsara hanyoyi da ababen hawa da kuma kula da gudun ababen hawa. Gabaki daya dai, babban burin shi ne samar da tsarin tsaro a fannin sufuri ba tare da asarar rayuka ko samun rauni ba, wanda zai amfanar da dukkan masu bin hanyoyi a Afirka. Marubucin, Gift Dumedah, dan asalin kasar Ghana ne wanda ya kware a fannin bincike, tare da mai da hankali kan ayyukan sufuri da shige da fice a Afirka.
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Bukatar sake aiki da shirin Vision Zero don ceton rayuka a titunan Afirka a 2024
Kiyaye haddura hakki ne da ya rataya kan masu amfani da tituna, da masu kula da titi, da masu ginawa da kula da tsarin hanyoyi, da kuma masu samar da agaji bayan hadari. Daga Gift Dumedah Shekarar 2024 ta zo kuma buri na farko da ya kamata Afirka ta sa a gaba shi ne dakatar da yawan mace-mace da...

A taƙaice
Kiyaye haddura hakki ne da ya rataya kan masu amfani da tituna, da masu kula da titi, da masu ginawa da kula da tsarin hanyoyi, da kuma masu samar da agaji bayan hadari. Daga Gift Dumedah Shekarar 2024 ta zo kuma buri na farko da ya kamata Afirka ta sa a gaba shi ne dakatar da yawan mace-mace da...
