الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Betta Edu: Bola Tinubu ya bayar da umarnin yin bincike a Ma'aikatar Jinkai kan zargin badakalar N585m

An yi ta ce-ce-ku-ce a Nijeriya bayan wasu takardu sun nuna cewa Ministar Jinkai Betta Edu ta bayar da umarni ga Akanta Janar ta kasar ta tura N585m ga asusun wata mata mai suna Onlyelu Bridget Mojso a matsayin tallafi. Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike a Ma'aik...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:08 ص
Betta Edu: Bola Tinubu ya bayar da umarnin yin bincike a Ma'aikatar Jinkai kan zargin badakalar N585m
لمحة سريعة

An yi ta ce-ce-ku-ce a Nijeriya bayan wasu takardu sun nuna cewa Ministar Jinkai Betta Edu ta bayar da umarni ga Akanta Janar ta kasar ta tura N585m ga asusun wata mata mai suna Onlyelu Bridget Mojso a matsayin tallafi. Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike a Ma'aik...

An yi ta ce-ce-ku-ce a Nijeriya bayan wasu takardu sun nuna cewa Ministar Jinkai Betta Edu ta bayar da umarni ga Akanta Janar ta kasar ta tura N585m ga asusun wata mata mai suna Onlyelu Bridget Mojso a matsayin tallafi. Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike a Ma'aikatar Jinkai wadda ke karkashin Betta Edu kan zargin badakalar miliyoyin kudade. Shugaban kasar ya bayar da umarnin ne ranar Lahadi da maraice, kamar yadda wata sanarwa da Ministan Watsa Labarai na kasar Mohammed Idris, ta sanar. An yi ta ce-ce-ku-ce a kasar bayan wasu takardu sun nuna cewa Ministar Jinkai Betta Edu ta bayar da umarni ga Akanta Janar ta Nijeriya ta tura naira miliyan 585 ga asusun wata mata mai suna Onlyelu Bridget Mojso a matsayin tallafi na shirin bayar da kudi ga marasa galihu. Sai dai Akanta Janar ta Nijeriya Dakta Oluwatoyin Madein ta ce ofishinta ba ya biyan kudi a madadin ma’aikatu da hukumomin gwamnati kan ayyukan da suke aiwatarwa. Dalilin da ya sa na yi watsi da bukatar Ministar Jinkai Betta Edu: Akanta Janar ta Nijeriya Hakan ya karfafa zargin da ake yi wa Betta Edu na yunkurin karkatar da kudaden gwamnati zuwa asusun daidaikun jama’a. Amma sanarwar da Ministan Watsa Labarai ya fitar ta ce gwamnati na sane da abin da ke faruwa a Ma'aikatar Jinkai kuma za ta yin cikakken bincike don gano hakikanin gaskiya. “A kan haka ne, shugaban kasa ya bayar da umarni a gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da gaskiya da sahihancin wadannan rahotanni,” in ji Mohammed Idris . Ya kara da cewa gwamnatin Shugaba Tinubu “tana gudanar da lamuranta a fayyace” don haka za ta dauki matakin da ya kamata idan ta gama bincikenta.