Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Bayanai kai-tsaye kan rikicin Iran da Isra'ila: Rahotanni sun ce Israi'la ta kai wa Iran hari da makamai masu linzami

Isra'ila ta kai harin makamai masu linzami a yankunan Iran, kamar yadda kafar watsa labarai ta ABC News ta ambato jami'an Amurka suna cewa, yayin da Fars News Agency na Iran ya ce an ji fashewar abubuwa a filin jirgin saman Isfahan. 0040 GMT — Isra'ila ta kai a Iran harin makamai masu linzami Isr...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:08
Bayanai kai-tsaye kan rikicin Iran da Isra'ila: Rahotanni sun ce Israi'la ta kai wa Iran hari da makamai masu linzami
Кратко

Isra'ila ta kai harin makamai masu linzami a yankunan Iran, kamar yadda kafar watsa labarai ta ABC News ta ambato jami'an Amurka suna cewa, yayin da Fars News Agency na Iran ya ce an ji fashewar abubuwa a filin jirgin saman Isfahan. 0040 GMT — Isra'ila ta kai a Iran harin makamai masu linzami Isr...

Isra'ila ta kai harin makamai masu linzami a yankunan Iran, kamar yadda kafar watsa labarai ta ABC News ta ambato jami'an Amurka suna cewa, yayin da Fars News Agency na Iran ya ce an ji fashewar abubuwa a filin jirgin saman Isfahan. 0040 GMT — Isra'ila ta kai a Iran harin makamai masu linzami Isra'ila ta kai a Iran harin makamai masu linzami, in ji ABC News , wanda ya ambato jami'an gwamnatin Amurka. Kazalika kamfanin dillancin labara na Fars news da ke Iran ya bayar da rahotanni fashewar wasu abubuwa a filin jirgin saman tsakiyar Isfahan, ko da yake ba a san dalilin aukuwar fashewar ba. "Har yanzu ba a san dalilin akuwar fashewar ba, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin tabbatar da musabbabin wannan lamari," in ji Fars news agency. An soma juya akalar jiragen fasinja ranar Juma'a da safe a yammacin Iran, a cewar kamfanin dillancin labarai na AP. A ƙarshen makkon jiya, Iran ta ƙaddamar da jerin hare-hare na ɗaruruwan makamai masu linzami da jirage maras matuƙa a Isra'ila don yin raddi kan harin da Isra'ila ta kai ƙaramin ofishin jakadancinta da ke Syria. A birnin Isfahan ne ake da manyan filayen jiragen saman sojin Iran, da kuma tashoshin nukiliyarta. Jami'an gwamnatin Iran ba su bayar da martani ba kawo yanzu. Isfahan na da nisan kilomita 350 daga Tehran, babban birnin Iran.