Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Bayanai kai-tsaye kan rikicin Iran da Isra'ila: Iran ta ce babu abin da ya sami tashoshin nukiliyarta da ke Isfahan

Isra'ila ta kai harin makamai masu linzami a yankunan Iran, kamar yadda kafar watsa labarai ta ABC News ta ambato jami'an Amurka suna cewa, yayin da Fars News Agency na Iran ya ce an ji fashewar abubuwa a filin jirgin saman Isfahan. 0448 GMT — Filayen jiragen saman Tehran sun ci gaba da aiki: Kam...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:08
Bayanai kai-tsaye kan rikicin Iran da Isra'ila: Iran ta ce babu abin da ya sami tashoshin nukiliyarta da ke Isfahan
Bu haberde ne var?

Isra'ila ta kai harin makamai masu linzami a yankunan Iran, kamar yadda kafar watsa labarai ta ABC News ta ambato jami'an Amurka suna cewa, yayin da Fars News Agency na Iran ya ce an ji fashewar abubuwa a filin jirgin saman Isfahan. 0448 GMT — Filayen jiragen saman Tehran sun ci gaba da aiki: Kam...

Isra'ila ta kai harin makamai masu linzami a yankunan Iran, kamar yadda kafar watsa labarai ta ABC News ta ambato jami'an Amurka suna cewa, yayin da Fars News Agency na Iran ya ce an ji fashewar abubuwa a filin jirgin saman Isfahan. 0448 GMT — Filayen jiragen saman Tehran sun ci gaba da aiki: Kamfanin labaran Iran Kamfanin dillancin labaran Iran ya ce filayen jiragen sama biyu na Tehran sun koma bakin aiki bayan da suka dakatar da aiki sakamakon ƙarar fashewar abubuwa da aka ji a tsakiyar Iran. "Jirage sun ci gaba da zirga-zirga a filayen Imam Khomeini da Mehrabad," a cewar kamfanin dillancin labarai na IRNA. 0424 GMT — Isra'ila ta umarci ofisoshin jakadancinta su yi gum da bakinsu kan harin da ta kai wa Iran Hukumomin Isra'ila sun umarci ofisoshin jakadancin da ke faɗin duniya su guje wa yin tsokaci game da harin da suka kai wa Iran, a cewar kafar watsa labarai ta Channel 12. 0304 GMT — Kafofin watsa labaran Iran sun ce babu abin da ya sami tashoshin nukiliyar Isfahan Kafafen watsa labaran Iran sun ce tashoshin nukiliya da ke kusa da birnin Isfahan na tsakiyar ƙasar suna "cikin tsaro" bayana an ji ƙarar fashewa a kusa da yankin da suke. "Tashoshin nukiliya da ke lardin Isfahan suna cikin tsaro," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito ina ya ambato wasu "sahihan majiyoyi". 0050 GMT — Iran ta musanta iƙirarin kai mata harin 'makamai masu linzami', ta ce ta lalata jirage 3 maras matuƙa na Isra'ila Wani jami'in gwamnatin Iran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa babu wani harin makamai masu linzami da aka kai a cikin ƙasarsu, yana mai ƙaryata rahotannin kafafen watsa labaran Amurka da ke cewa Isra'ila ta kai musu hari. An ambato kakakin hukumar kula da sararin samaniyar Iran yana cewa ba a kai musu harin makamai masu linzami ba, inda ya ƙara da cewa na'urorinsu sun kakkaɓo jirage maras matuƙa da dama daga sararin samaniyar yankin Isfahan. Sai dai jami'an gwamnatin Amurka biyu sun tabbatar wa CBS News cewa wani makami mai linzami na Isra'ila ya sauka a Iran. Reuters ya ruwaito cewa Isra'ila ta gaya wa Amurka shirinta na kai wa Iran hari. Wasu jami'an gwamnatin Amurka da ba sa so a ambace su sun shaida wa CBS News cewa Isra'ila ta yi amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango a harin da ta kai wa Iran. Wani jami'in Amurka ya shaida wa CNN cewa mahukunta a Washington ba su "amince" Isra'ila ta kai harin ba. "Ba mu amince a mayar da martani ba," a cewar jami'in gwamnatin Amurka. Jami'in ya tabbatar da cewa Isra'ila ta shaida wa Amurka cewa za ta kai wa Iran hari nan da kwanaki masu zuwa. Jagoran Addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya ce dole su hukunta Isra'ila bayan harin da ta kai ofishin jakadancinsu da ke Damascus a farkon watan Afrilu / Hoto: Reuters 0040 GMT — Isra'ila ta kai wa Iran harin makamai masu linzami Isra'ila ta kai wa Iran harin makamai masu linzami, in ji ABC News , wanda ya ambato jami'an gwamnatin Amurka. Kazalika kamfanin dillancin labarai na Fars news da ke Iran ya bayar da rahotannin fashewar wasu abubuwa a filin jirgin saman tsakiyar Isfahan, ko da yake ba a san dalilin aukuwar fashewar ba. "Har yanzu ba a san dalilin aukuwar fashewar ba, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin tabbatar da musabbabin wannan lamari," in ji Fars news Agency. An soma juya akalar jiragen fasinja ranar Juma'a da safe a yammacin Iran, a cewar kamfanin dillancin labarai na AP. A ƙarshen makon jiya, Iran ta ƙaddamar da jerin hare-hare na ɗaruruwan makamai masu linzami da jirage maras matuƙa a Isra'ila don yin raddi kan harin da Isra'ila ta kai ƙaramin ofishin jakadancinta da ke Syria. A birnin Isfahan ne ake da manyan filayen jiragen saman sojin Iran, da kuma tashoshin nukiliyarta. Jami'an gwamnatin Iran ba su bayar da martani ba kawo yanzu. Isfahan na da nisan kilomita 350 daga Tehran, babban birnin Iran. A birnin Isfahan ne ake da manyan filayen jiragen saman sojin Iran, da kuma tashoshin nukiliyarta. / Hoto: TRT World 2240 GMT — Amurka da Birtaniya sun sanar da sanya wa Iran jerin takunkumai kan harin da ta kai wa Isra'ila Amurka da Birtaniya sun sanar da sanya wa Iran jerin takunkumai a fannin jirage maras matuƙa na sojinta sakamakon harin da ta kai wa Isra'ila da makamai masu linzami da jirage maras matuƙa a ƙarshen mako. "A yau, za mu ɗauki mataki kan Iran — za mu sanya mata sabbin takunkumai da taƙaita abubuwan da za ta fitar ƙasashen waje," a cewar shugaban Amurka Joe Biden a wata sanarwa da ya fitar. "Harin da gwamnatin Iran ta kai wa Isra'ila na ganganci ne kuma yana da hatsari na watsuwar rikici," in ji Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak, inda ya ƙara da cewa Birtaniya ta sanya takunkumai kan "shugabannin sojoji da rundunonin tsaron Iran waɗanda suke da nauyin kai harin ƙarshen mako." Iran ta ƙaddamar da hari kai-tsaye karon farko zuwa cikin Isra'ila ranar Asabar domin yin martani kan harin da Isra'ila ta kai a ofishin jakadancinta da ke Damascus ranar 1 ga watan Afrilu inda ta kashe zaratan sojojin runduna ta musamman ta Islamic Revolutionary Guard Corps, ciki har da janar guda biyu.