Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Bankin Musulunci zai ba da dala miliyan $418 ga Tajikistan, Benin, Ivory Coast, da Turkiyya

Bankin Musulunci na Raya Ƙasa (IsDB) ya amince ya bai wa ƙasashe huɗu kuɗaɗe don ayyukan cigaba, wanda ya kai dala miliyan $418, ga Tajikistan, Benin, Ivory Coast, da Turkiayya. Bankin Musulunci na Raya Cigaban Tattalin Arziƙi (IsDB) ya amince da bayar da dala miliyan $418 domin ayyukan cigaba a...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:08
Bankin Musulunci zai ba da dala miliyan $418 ga Tajikistan, Benin, Ivory Coast, da Turkiyya
En bref

Bankin Musulunci na Raya Ƙasa (IsDB) ya amince ya bai wa ƙasashe huɗu kuɗaɗe don ayyukan cigaba, wanda ya kai dala miliyan $418, ga Tajikistan, Benin, Ivory Coast, da Turkiayya. Bankin Musulunci na Raya Cigaban Tattalin Arziƙi (IsDB) ya amince da bayar da dala miliyan $418 domin ayyukan cigaba a...

Bankin Musulunci na Raya Ƙasa (IsDB) ya amince ya bai wa ƙasashe huɗu kuɗaɗe don ayyukan cigaba, wanda ya kai dala miliyan $418, ga Tajikistan, Benin, Ivory Coast, da Turkiayya. Bankin Musulunci na Raya Cigaban Tattalin Arziƙi (IsDB) ya amince da bayar da dala miliyan $418 domin ayyukan cigaba a Tajikistan da Benin, Ivory coast da Turkiyya. Kwamitin zartarwa na bankin ya sahale da aiwatar da ayyukan huɗu yayin taronsa karo na 355 l, wanda ya mayar da hankali kan cigaban zamantakewa da tattalin arziƙi. Bankin ya sanar a taronsa na shekara-shekara, wanda ya zo daidai da cikarsa shekaru 50, a babban birnin Saudiyya, Riyadh. Tajikistan za ta samu dala miliyan $150 don gina tashar lantarki ta Rogun Lot-4, don samar da makamashin lantarki mai tsafta da ƙasar za ta iya dogara a kai. Benin za ta samu Euro miliyan €60.6 (dala miliyan $65) don cigaban harkar noman rogo, wanda zai haɓaka wadatar abinci da samar da kuɗaɗe ga al'ummar ƙasar. Shirin zai kuma inganta tattalin arziƙi da ƙarfin sarrafa kayan noma, da shigowar fannin kamfanoni masu zaman kansu a harkar sarrafa rogo, dankali, da doya. Ivory coast za ta samu Euro miliyan €70.56 (dala miliyan $75.5) na kuɗaɗe don haɓaka fannin noman rogo, don wadatar da ƙasa da abinci, da ɗaukaka tattalin arziƙi da samar da kuɗin shiga ga mutane ta hanyar noman rogo, da sarrafa shi da haɗin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu. Kwamitin ya amince da Euro miliyan €120 (dala miliyan $128.5) ga Turkiyya don aikin babban titin Nakkas-Basaksehir, wanda zai kasance wani yanki na babban titin Arewacin Marmara ƙarƙashin shirin gwamnatin ƙasar. Bankin ya ce game da aikin cigaba a Turkiyya, "Babbar manufar aikin shi ne samar da wata mashiga, ƙari kan titin tsallaka Bosphorus, don rage yawan ababen hawa da tsaiko, da rage lokacin tafiya, da yawan fitar da iskar gas mai gurɓata muhalli".