Shugaban rukunin kamfanonin na Dangote ya nemi ƴan ƙasar nan da su yi watsi da labarin, inda ya yi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Nijeriya. Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nesanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi ‘yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa. Dangote ya ce “wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin ɓata masa suna, a daidai lokacin da ƴan Nijeriya ke cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi saboda wahalhalun da ake fama da su,” kamar yadda sanarwar da kamfaninsa ya fitar ta bayyana. Shugaban rukunin kamfanonin na Dangote ya nemi ƴan ƙasar nan da su yi watsi da labarin, inda ya yi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Nijeriya. "Duk abin da ya shafi yan Najeriya ya shafe mu", in ji sanarwar. Matsalar hauhawar farashi da tsadar rayuwa da matsi na ci gaba da ta’azzara a Nijeriya, inda har a makon da ya wuce wasu al’umma suka yi zanga-zanga a jhar Neja da nufin jawo hankalin gwamnati kan lamarin. Sai dai gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi suna ta lallashin ƴan ƙasar tare da alkawarta musu cewa abubuwa za su yi sauki ba da jimawa ba. A sanarwar kamfanin nasa, Dangote ya ƙara da cewa, ''an kawo maganar faɗuwar darajar Naira da sayen kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na ƙashin kai bukatun da ba a samu damar biya ba a baya." "Muma muna sayen muhimman kayan abinci a kasuwa kamar yadda kowa ke saya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen ciyar da al'umma," in ji Dangote. Shugaban kamfanin ya kuma bayyana mamaki kan yadda ake neman haddasa saɓani tsakanin Kamfanin Dangote da gwamnatin tarayya, inda ya ce shi ɗan kasuwa ne ba ɗan siyasa ba, don haka babu inda ya yi maganar ƙalubalantar gwamnati. "Kamfaninmu ya kasance mai bin dokokin ƙasa a ko da yaushe, tare da neman sauƙi ga al'umma da fatan alheri." Sanarwar ta nemi ƴan Nijeriya da su guji ɗaukar saƙon da ba daga kamfani ya fito ba kai tsaye, tare da guje wa yaɗa jita-jita.
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Ban ce na fi ƴan Nijeriya shan wahalar tsadar rayuwa ba —Dangote
Shugaban rukunin kamfanonin na Dangote ya nemi ƴan ƙasar nan da su yi watsi da labarin, inda ya yi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Nijeriya. Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nesanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani...

Shugaban rukunin kamfanonin na Dangote ya nemi ƴan ƙasar nan da su yi watsi da labarin, inda ya yi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Nijeriya. Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nesanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani...
