Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Babban martanin da Isra'ila za ta gani kan kisan ƙare dangi a Gaza zai zo ne daga Turkiyya : Erdogan

Birnin Ƙudus namu ne har abada, kuma ba za a sake raba shi ba,” yana mai jaddada cewa ba za a taba kafa wata ƙasa ta Falasɗinu ba. Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan a ranar Alhamis ya bayyana cewa shirye-shiryen da ake yi na “jefa yankinmu cikin rashin kwanciyar hankali” ba za su yi nasara...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:08
Babban martanin da Isra'ila za ta gani kan kisan ƙare dangi a Gaza zai zo ne daga Turkiyya : Erdogan
Bu haberde ne var?

Birnin Ƙudus namu ne har abada, kuma ba za a sake raba shi ba,” yana mai jaddada cewa ba za a taba kafa wata ƙasa ta Falasɗinu ba. Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan a ranar Alhamis ya bayyana cewa shirye-shiryen da ake yi na “jefa yankinmu cikin rashin kwanciyar hankali” ba za su yi nasara...

Birnin Ƙudus namu ne har abada, kuma ba za a sake raba shi ba,” yana mai jaddada cewa ba za a taba kafa wata ƙasa ta Falasɗinu ba. Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan a ranar Alhamis ya bayyana cewa shirye-shiryen da ake yi na “jefa yankinmu cikin rashin kwanciyar hankali” ba za su yi nasara ba, kuma “masu zubar da jini na mulkin mallaka da aƙidar tsananin son kafa ƙasar Isra’ila” ba za su cim ma burinsu ba. “Martani mafi ƙarfi ga wannan kisan kare dangi da aka shaida na tsawon watanni 23 da dukkan bil’adama zai fito ne daga Turkiyya da al’ummarta,” in ji Erdogan yayin bikin raba guraben aiki ga dangin shahidai, jarumai, da danginsu a hukumomin gwamnati a Ankara. “Mun mulki kasashen da ke kalubalantar mu tsawon ɗaruruwan shekaru wadanda su kuma a gomman shekarun baya bayan nan suka samu,” in ji Shugaban Turkiyya, yana mai jaddada cewa, “Mun kasance takobin adalci, muna kawo tsari ga duniya.” “Mu ba baƙi ba ne ko masu mamaye wannan yanki; mun kasance masu masaukinsa tsawon shekaru dubu kuma za mu ci gaba da kasancewa nan har abada,” Erdogan ya ƙara da cewa. Erdogan ya mayar da martani ga Netanyahu Maganganun Erdogan na baya-bayan nan sun kasance martani ga rikicin kalamai tsakaninsa da Netanyahu, wanda ya fara ne lokacin da shugaban Isra’ila ya ambaci sunan Erdogan yayin wani biki a yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, tare da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio da Jakadan Mike Huckabee a ranar Litinin.