Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 119 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 27,131 sannan suka jikkata mutum 66,287, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 1811 GMT –– Babban jami'in MDD ya damu da yiwuwar kai farmakin da Isra'ila ke yi a Rafah Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nuna matukar damuwa kan yiwuwar fadada hare-haren da sojojin Isra'ila ke kaiwa Rafah a kudancin Gaza, in ji kakakinsa. "Mun riga mun ga tasirin farar hula tare da ayyukan da aka yi a Khan Younis, ba kawai tasiri ba har ma da tasirin da ke kan gininmu lokacin da aka kai hari a gidanmu." Stephane Dujarric ya shaida wa manema labarai a birnin New York cewa, "Tabbas, tun farkon fara kai hare-hare ta ƙasa, mutane suna ta rububin komawa kudanci." Ya kara da cewa akwai “cunkoson mutane” a kudu kuma mutane suna rayuwa cikin “mummunan yanayi” a can. "Don haka, hakika abin akwai matukar damuwa," in ji shi. 1301 GMT –– Hamas ta tsaya tsayin daka kan bukatar tsagaita wuta ta dindindin Jami'an Hamas sun ce kungiyar na nazari kan shirin tsagaita wuta da ake shirin yi wanda zai hada da dogon lokaci na dakatar da yaƙin Gaza da kuma musayar fursunoni, amma ga alama kungiyar ta kawar da wasu muhimman abubuwan da ta shirya. Osama Hamdan, wani babban jami'in Hamas a Beirut, ya ce kungiyar ta ci gaba da jajircewa kan bukatunta na farko na tsagaita wuta na dindindin. Hamdan ya kuma ce kungiyar na neman a sako dubban fursunonin Falasdinawan da ake tsare da su bisa aikata laifukan da suka shafi rikici da Isra'ila, ciki har da wadanda ke zaman ɗaurin rai da rai. Ya ambaci sunayen mutum biyu da suka hada da Marwan Barghouti, shahararren jagoran bore na Falasdinu. 1154 GMT –– Falasɗinawa 112 aka kashe a Gaza cikin awa 24 Falasɗinawa 112 aka kashe a Gaza cikin awa 24 / Photo: AFP Akalla Falasdinawa 112 ne suka mutu yayin da wasu 148 suka jikkata a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a Zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya, in ji Ma'aikatar Lafiya ta yankin. A cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta ce: "Isra'ila ta yi wa wasu iyalai 'yan gida ɗaya su 13 kisan kiyashi 13 a Gaza, inda mutum 112 suka rasa rayukansu tare da jikkata 148 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata. Sanarwar ta ce "Mutane da yawa har yanzu suna maƙale a karkashin ɓaraguzan gine-gine da kuma kan tituna yayin da masu aikin ceto ba su iya isa gare su," in ji sanarwar. Duk da hukuncin wucin gadi na Kotun Duniya, Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare kan Gaza inda aka kashe aƙalla Falasdinawa 27,131, galibi mata da yara, yayin da 66,287 suka jikkata tun ranar 7 ga Oktoba, a cewar hukumomin lafiya na Falasdinu.
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Babban jami'in MDD ya damu da yiwuwar kai farmakin da Isra'ila ke yi a Rafah
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 119 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 27,131 sannan suka jikkata mutum 66,287, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 1811 GMT –– Babban jami'in MDD ya damu da yiwuwar kai farmakin da Isra'ila ke yi...

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 119 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 27,131 sannan suka jikkata mutum 66,287, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 1811 GMT –– Babban jami'in MDD ya damu da yiwuwar kai farmakin da Isra'ila ke yi...
