Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Babban jami'in Binance ya tsere daga hannun jami'an tsaron Nijeriya

Ofishin Babban Mai Bai Wa Shugaban Nijeriya Shawara Kan Harkokin Tsaro ne ya tabbatar da tserewarsa a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin. Shugaban kamfanin hada-hadar kuɗaɗe na Binance reshen Afirka ya tsere daga hannun jami’an tsaron da yake tsare a wurinsu. Ofishin Babban Mai Bai Wa Shuga...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:08
Babban jami'in Binance ya tsere daga hannun jami'an tsaron Nijeriya
At a glance

Ofishin Babban Mai Bai Wa Shugaban Nijeriya Shawara Kan Harkokin Tsaro ne ya tabbatar da tserewarsa a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin. Shugaban kamfanin hada-hadar kuɗaɗe na Binance reshen Afirka ya tsere daga hannun jami’an tsaron da yake tsare a wurinsu. Ofishin Babban Mai Bai Wa Shuga...

Ofishin Babban Mai Bai Wa Shugaban Nijeriya Shawara Kan Harkokin Tsaro ne ya tabbatar da tserewarsa a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin. Shugaban kamfanin hada-hadar kuɗaɗe na Binance reshen Afirka ya tsere daga hannun jami’an tsaron da yake tsare a wurinsu. Ofishin Babban Mai Bai Wa Shugaban Nijeriya Shawara Kan Harkokin Tsaro ne ya tabbatar da tserewarsa a wata sanarwar da ya fitar a ranar Litinin. Nadeem Anjarwalla, wanda ke da fasfon Birtaniya da Kenya, shi ne manajan Binance a yankin Afirka, ya tsere ne daga wurin da yake tsare a ranar Juma’a, kamar yadda sanarwar ta tabbatar. Haka kuma ta ce jami’an tsaron Nijeriya na aiki da ƴan sandan ƙasa da ƙasa domin samun takardar sammacin wadda za ta kai ga kama Mista Anjarwalla.