Shugabannin ƙungiyar ne suka bayyana haka jim kaɗan bayan sun fito daga taron da suka gudanar da shugaban majalaisar dattawan Nijeriya Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilan ƙasar Tajuden Abbas, wanda da alama bai cim ma wata nasara ba. Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta ce ba za ta fasa yajin aikin da ta ƙuduri aniyar tsunduma ranar Litinin ba game da buƙatarta wajen gwamnatin ƙasar kan ƙarin albashi mafi ƙaranci ga ma'aikatan ƙasar. Shugabannin ƙungiyar ne suka bayyana haka jim kaɗan bayan sun fito daga taron da suka gudanar ranar Lahadi da daddare da shugaban majalisar dattawan Nijeriya Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilan ƙasar Tajuden Abbas don samun bakin-zaren, wanda da alama bai cim ma wata nasara ba. “A halin da ake ciki, ba mu da ikon yanjewa daga yajin aikin da za a soma ranar Litinin da safe, za a tafi yajin aikin a yayin da za mu gabatar da roƙon da shugabbanin Majalisar dokokin ƙasar suka yi ga rassanmu daban-daban, a kan kiran da suka yi na mu janye yajin aikin” in ji shugaban ƙungiyar TUC Festus Osifo, bayan sun fito daga taron. Ƙungiyoyin Ƙwadagon sun yanke shawarar tafiya yajin aiki ne bayan sun kasa samun matsaya da gwamnatin tarayya kan mafi ƙarancin albashi da kuma buƙatarsu ta neman a janye ƙarin da aka yi na kuɗin lantarki a faɗin ƙasar.
Архив новостей
В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.
Ba za mu fasa yajin aiki a Nijeriya ba - NLC
Shugabannin ƙungiyar ne suka bayyana haka jim kaɗan bayan sun fito daga taron da suka gudanar da shugaban majalaisar dattawan Nijeriya Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilan ƙasar Tajuden Abbas, wanda da alama bai cim ma wata nasara ba. Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta ce ba za ta fas...

Кратко
Shugabannin ƙungiyar ne suka bayyana haka jim kaɗan bayan sun fito daga taron da suka gudanar da shugaban majalaisar dattawan Nijeriya Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilan ƙasar Tajuden Abbas, wanda da alama bai cim ma wata nasara ba. Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta ce ba za ta fas...
