Da yake tsokaci kan tattaunarsa da Shugaban Ghana John Mahama, Shugaba Tinubu ya ce shi ya yi murna matuƙa game da ƙoƙarin da Shugaba Mahama ya yi. Shugaban Nijeriya, Bola Hmed Tinubu, ya ce ba laifi ba ne idan aka samu mai shiga tsakanin ƙasashen AES na Nijar da Mali da Burkina Faso da ƙungiyar raya tattalin arziƙin yammacin Afirka, ECOWAS. Tinubu ya faɗi haka ne a fadar gwamnatin Nijeriya da ke Abuja, bayan shugaban ƙasar Ghana, John Mahama, ya ba shi labarin tuntuɓar sulhu da ya yi da shugabannin ƙasashen AES ɗin. Shugaban John Mahama ya ce matsalar rashin jituwar ƙasashen da ECOWAS aba ce mai sarƙaƙiya wadda ke buƙatar ƙarin tattaunawa. “Abubuwa biyu ne suka sa na kawo [ziyara]; na farko domin na gode masa [Shugaba Tinubu] bisa karramawar da ya yi mini lokacin bikin rantsar da ni. Kazalika na yi masa bayani game da ziyarar da na kai ƙasashen yankin Sahel- Burkina Faso da Mali da Nijar,” in ji Mahama. Har wa yau shugaban na Ghana ya shaida wa manema labarai a Abuja cewa shi ya yi wa shugaba Tinubu bayani game da tattaunawarsa da shugabannin ƙasashen na AES. “A matsayinsa na shugaban ECOWAS nauyi ne da ya rataya a kaina na zo na yi masa karin bayani game da wasu daga cikin ƙorafe-ƙorafe da aka nuna a can ta yadda za mu ga hanyoyin da za a ci gaba da tattaunawa da waɗancan ƙasashe,” a cewar Mahama. “Lamari ne mai sarƙaƙiya ba abu ne mai sauƙi kamar yadda muke tunani ba Amma ya kamata mu ci gaba da tattaunawa domin ganin yadda za mu haɗa kai tare,” in ji shi. Da yake tsokaci kan tattaunarsa da Shugaban Ghana John Mahama, Shugaba Tinubu ya ce shi ya yi murna matuƙa game da ƙoƙarin da Shugaba Mahama ya yi. "Ba laifi ba ne a gare mu a samu mai shiga tsakanin ƙasashen AES da ƙungiyar ECOWAS saboda rashin tsaron da ake da shi a yankin Sahel...Mutanen da ba su ji ba ba su gani ba na waɗancan kasashe su ne lamarin ya fi shafa, ba mu shugabanni ba,” in ji Shugaba Tinubu. Ɓaraka a ECOWAS Ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso dai sun fice ne daga ƙungiyar ECOWAS sakamakon barazanar mayar da hamɓararriyar gwamnatin Mohamed Bazoum da ƙarfin tuwo kan mulki a Nijar da ECOWAS ta yi bayan an yi masa juyin mulki. A wancan ƙasashen Mali da Burkina Faso sun ce idan aka kai hari a Nijar su ma za su mayar da martani. ECOWAS dai ta ƙaƙaba wa Nijar takunkumi domin ganin an mayar da Bazoum kan, mulki. Maimakon sakewa tare da mayar da Bazoum ɗin kan mulki sai Nijar tare da ƙasashen Mali da Burkina Faso suka yi shelar ficewarsu daga ECOWAS. Daga baya ECOWAS ta cire takunkumin da ta ƙaƙaba wa Nijar, sai dai wannna matakin bai hana ƙasashen kafa wata ƙungiyar haɗaka mai suna AES ba. Kana ECOWAS ta tura shugaban ƙasar Senegal Bassirou Faye domin shawao kan ƙasashen na AES. Sai dai wannan matakin na tura shugaban Senegal ɗin bai yi nasarar shawo ƙasashen AES ba.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Ba laifi ba ne idan aka samu mai shiga tsakanin AES da ECOWAS— Tinubu
Da yake tsokaci kan tattaunarsa da Shugaban Ghana John Mahama, Shugaba Tinubu ya ce shi ya yi murna matuƙa game da ƙoƙarin da Shugaba Mahama ya yi. Shugaban Nijeriya, Bola Hmed Tinubu, ya ce ba laifi ba ne idan aka samu mai shiga tsakanin ƙasashen AES na Nijar da Mali da Burkina Faso da ƙungiyar...
At a glance
Da yake tsokaci kan tattaunarsa da Shugaban Ghana John Mahama, Shugaba Tinubu ya ce shi ya yi murna matuƙa game da ƙoƙarin da Shugaba Mahama ya yi. Shugaban Nijeriya, Bola Hmed Tinubu, ya ce ba laifi ba ne idan aka samu mai shiga tsakanin ƙasashen AES na Nijar da Mali da Burkina Faso da ƙungiyar...
