Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Atiku ya soki Tinubu kan batun tsaro da tattalin arzikin Nijeriya

Atiku Abubakar ya zargi Shugaba Tinubu da tsayawa wasa da kuma tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje yayin da ƙasar ke fama da rashin tsaro. Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya caccaki Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu kan kamun ludayinsa dangane da mulkin Nijeriya. Atiku ya bayyan...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:08
Atiku ya soki Tinubu kan batun tsaro da tattalin arzikin Nijeriya
Kwa muhtasari

Atiku Abubakar ya zargi Shugaba Tinubu da tsayawa wasa da kuma tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje yayin da ƙasar ke fama da rashin tsaro. Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya caccaki Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu kan kamun ludayinsa dangane da mulkin Nijeriya. Atiku ya bayyan...

Atiku Abubakar ya zargi Shugaba Tinubu da tsayawa wasa da kuma tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje yayin da ƙasar ke fama da rashin tsaro. Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya caccaki Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu kan kamun ludayinsa dangane da mulkin Nijeriya. Atiku ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X inda ya zargi shugaban da gazawa wurin jagorancin ƙasar. “Tinubu ya tsaya wasa yayin da Nijeriya ke neman nutsewa cikin kogin rashin tsaro. A yi tunanin cewa babban kwamandan askarawa na ziyara wadda ba ta aiki ba a yayin da masu garkuwa da mutane suka kashe mace mai shayarwa da wata kaka a Abuja kan gaza biyan kuɗin fansa har miliyan 90 da kuma wasu sarakai biyu a Ekiti, da wasu bala’o’i da ke faruwa a Nijeriya,” in ji Atiku. “Idan takalman Emilokan sun yi masa girma, ya janye gefe. Nijeriya ba ta buƙatar shugaba ɗan yawon buɗe ido. Kasar na bukatar shugabanci na awa 24 don tunkarar matsalar tsaro da tabarbarewar tattalin arziki, “ kamar yadda Atiku ya ƙara da cewa. Sai dai fadar shugaban Nijeriyar ba ta mayar da martani kan zargin da Atiku yake yi wa shugaba Tinubun ba.