Tsawon kwanaki 135, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 28,985 da raunata mutum 68,883 1605 GMT — Asibiti na biyu mafi girma a Gaza ya daina aiki Asibiti na biyu mafi girma a Gaza “ya daina aiki baki ɗaya”, kamar yadda mai magana da yawun Ma’akatar Lafiya ta Falasɗinu a Gaza ya tabbatar. “Ma’aikatan asibiti huɗu ne kacal ke kula da marasa lafiya” a cikin asibitin Al Nasser da ke kudancin birnin Khan Younis, in ji Ashraf al Qidra a tattaunawarsa da kamfanin dillancin labarai na Reuters. “Asibitin Nasser shi ne ƙashin bayan kiwon lafiya a kudancin Gaza. Daina aikin da ya yi tamkar hukuncin kisa ne ga dubu ɗaruruwan Falasɗinawan da suka rasa muhallansu a Khan Younis da Rafah,” a cewarsa. 0957 GMT — Hezbollah ta kai wa sojojin Isra'ila hari a wurare shida da ke kudancin Lebanon Ƙungiyar Hezbollah ta kai hare-hare a wurare shida da sojojin Isra’ila ke zama a kudancin Lebanon. A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce ta kai hari a wurare biyu a Gonakin Shebaa wanda ke ƙarƙashin Isra’ila da sansanin sojin Ramya. Haka kuma ta ce ta kai wasu hare-haren a Burket Risa da Ed-Dahira da kuma sansanin Beranit. Isra'ila ta mamaye Gonakin Shebaa da tsaunin Kefr Shuba da wani yanki na kauyen Gacar na Lebanon lokacin da ta mamaye yankin Tuddan Golan na Syria a shekarar 1967. 0935 GMT — Ƙasashen duniya na ƙara matsa wa Isra'ila lamba kan ta bi umarnin Kotun Duniya Ministan Harkokin Wajen Portugal Joao Gomes Cravinho ya nuna matuƙar damuwa a yayin taro kan tsaro da aka yi a Munich dangane da yadda Gaza ke ƙara faɗawa cikin bala’i da neman agaji. Cravinho ya buƙaci Isra’ila da ta bi dokokin ƙasa da ƙasa inda ya ce akwai buƙatar ta bi umarnin Kotun Duniya. A ɗayan ɓangaren kuwa, babban jami’in diflomasiyya na ƙasar Malta Ian Borg ya yi Allah wadai da kisan da Isra’ila ke yi wa farar hula, musamman dangane da mayar da martani kan harin 7 ga watan Oktoba. Borg ya yi kira da a gaggauta tsagaita wuta kuma tsagaita wutar ta kasance ta dindindin. Duk da ya goyi bayan Isra’ila ta kare kanta, ya jaddada muhimmancin mayar da martani daidai gwargwado ga abubuwan da suka faru.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Asibiti na biyu mafi girma a Gaza ya daina aiki
Tsawon kwanaki 135, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 28,985 da raunata mutum 68,883 1605 GMT — Asibiti na biyu mafi girma a Gaza ya daina aiki Asibiti na biyu maf...

Tsawon kwanaki 135, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 28,985 da raunata mutum 68,883 1605 GMT — Asibiti na biyu mafi girma a Gaza ya daina aiki Asibiti na biyu maf...
