Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Ƙaruwar cutar kwalara na da alaƙa da sauyin yanayi - WHO

Masana sun yi gargaɗi kan cewa ana samun ƙaruwar ɓarkewar cutar kwalara kuma hakan na da alaƙa sosai da sauyin yanayi da kuma halin da ake ciki a wuraren da ake yaƙi. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da cewa cutar amai da gudawa ta kwalara na da alaƙa mai ƙarfi da matsalolin sauyin yanayi. D...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:08
Ƙaruwar cutar kwalara na da alaƙa da sauyin yanayi - WHO
Bu haberde ne var?

Masana sun yi gargaɗi kan cewa ana samun ƙaruwar ɓarkewar cutar kwalara kuma hakan na da alaƙa sosai da sauyin yanayi da kuma halin da ake ciki a wuraren da ake yaƙi. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da cewa cutar amai da gudawa ta kwalara na da alaƙa mai ƙarfi da matsalolin sauyin yanayi. D...

Masana sun yi gargaɗi kan cewa ana samun ƙaruwar ɓarkewar cutar kwalara kuma hakan na da alaƙa sosai da sauyin yanayi da kuma halin da ake ciki a wuraren da ake yaƙi. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da cewa cutar amai da gudawa ta kwalara na da alaƙa mai ƙarfi da matsalolin sauyin yanayi. Dakta Kate O’Brien wadda ita ce daraktar rigakafi ta hukumar, ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai. “Ina ganin ya kamata mu san cewa ɓarkewar cutar kwalara da ake fama da ita na da alaƙa da sauyin yanayi, kuma mun ankarar dangane da kwalara,” in ji O’Brien. “Ba wai batun rigakafi ne kaɗai ba, a gaskiya ba ita ce kaɗai hanyar farko ta kariya daga kwalara ba. Kwalara cuta ce da ke da alaƙa da tsaftar ruwa da tsaftar muhalli. Kuma rigakafi hanya ce ta kiyaye cuta idan akwai ta.” Haka kuma O’Brien ta bayyana cewa a halin yanzu duniya na shirin fuskantar ɓarkewar cutar ƙyanda. “Sakamakon ɓarkewar cututtuka da ake samu, sauyin yanayi da ƙaruwar jama’a da matsalolin ayyukan jin ƙai, batun kiyaye cututtuka ta hanyar rigakafi ba zai zama lamari mai muhimmanci ba a yanzu,” in ji ta.