Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Ɓangarorin da ke yaƙi da juna a Sudan sun haɗu a Geneva don tattaunawar tsagaita wuta da MDD ta shirya

Tun watan Afrilun 2023 ne ake ta gwabza yaƙi tsakanin Sojojin Sudan da Dakarun sa kai na RSF a ƙasar, lamarin da ya raba kusan mutane miliyan 10 da mastugunansu tare da jefa su cikin barazanar haɗarin yunwa. Ɓangarorin da ke rikici da juna a Sudan sun isa birnin Geneva na ƙasar Switzerland domin...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:08
Ɓangarorin da ke yaƙi da juna a Sudan sun haɗu a Geneva don tattaunawar tsagaita wuta da MDD ta shirya
Kwa muhtasari

Tun watan Afrilun 2023 ne ake ta gwabza yaƙi tsakanin Sojojin Sudan da Dakarun sa kai na RSF a ƙasar, lamarin da ya raba kusan mutane miliyan 10 da mastugunansu tare da jefa su cikin barazanar haɗarin yunwa. Ɓangarorin da ke rikici da juna a Sudan sun isa birnin Geneva na ƙasar Switzerland domin...

Tun watan Afrilun 2023 ne ake ta gwabza yaƙi tsakanin Sojojin Sudan da Dakarun sa kai na RSF a ƙasar, lamarin da ya raba kusan mutane miliyan 10 da mastugunansu tare da jefa su cikin barazanar haɗarin yunwa. Ɓangarorin da ke rikici da juna a Sudan sun isa birnin Geneva na ƙasar Switzerland domin tattaunawa kan ''yiwuwar tsagaita wuta a kasar'' wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta shirya da nufin sauƙaƙa ayyukan jin kai da kare fararen hula, in ji mai magana da yawun MDD. Yaƙin Sudan, wanda ya ɓarke a watan Afrilun 2023 ya tilasta wa mutane kusan miliyan 10 barin matsugunansu, lamarin da ya haddasa barazanar yunwa da rikice-rikice na ƙabilanci waɗanda aka ɗora alhakinsa kan ƙungiyar Rapid Support Forces (RSF). Yarjejeniyar da aka ƙulla a birnin Jeddah na ƙasar Saudiyya tsakanin Sojojin Sudan da dakarun sa kai na RSF wacce Amurka da Saudiyya suka jagoranta a ƙarshen shekarar bara ta wargaje. ''Zaman tattaunawar zai mayar da hankali ne kan lalubo hanyoyin ci gaba da ayyukan jin kai da kuma kare fararen hula ta hanyar tsagaita wuta a ƙasar, kamar yadda Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya buƙata,'' a cewar mai magana da yawun MDD sa'ilin da take amsa tambayoyin kamfanin dillancin labarai na Reuters. A cewarta, wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan Ramtane Lamamra daga Aljeriya ne ya shirya zaman tattaunawar da aka soma a ranar Alhamis. Sojojin Sudan da dakarun RSF za su yi zaman "tattaunawa" ta hanyar masu shiga tsakani a maimakon ganawa ido da ido, in ji ta. Jakadiyar Amurka a MDD Linda Thomas-Greenfield ta shaida wa gidan talabijin na CBS cewa, an gayyaci wakilin Amurka na musamman a Sudan Tom Perriello don shi ma yana daga masu zaman tattaunawar a Geneva wanda ya mayar da hankali kan ''yadda za a magance barazanar da ayyukan jin ƙai ke fuskanta da taimaka wa mabuƙata da nemo mafita kan matsalar siyasa domin haɗa ɓangarorin biyun da ke yaƙi da juna wuri guda.''