الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Ana zargin tsohon firaiministan Sudan Hamdok da laifin 'tunzura' mutane su yi yaƙi

Mutane goma sha biyar, ciki har da ƴan jarida da ƴan siyasa suna fuskantar irin wannan zargi. Ofishin mai shigar da ƙara na Sudan ya zargi tsohon firaiministan ƙasar Abdalla Hamdok da laifin "tunzura" mutane domin su "yaƙi ƙasar" da kuma wasu laifuka da ka iya jawowa a yanke wa mutum hukuncin kis...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:08 ص
Ana zargin tsohon firaiministan Sudan Hamdok da laifin 'tunzura' mutane su yi yaƙi
لمحة سريعة

Mutane goma sha biyar, ciki har da ƴan jarida da ƴan siyasa suna fuskantar irin wannan zargi. Ofishin mai shigar da ƙara na Sudan ya zargi tsohon firaiministan ƙasar Abdalla Hamdok da laifin "tunzura" mutane domin su "yaƙi ƙasar" da kuma wasu laifuka da ka iya jawowa a yanke wa mutum hukuncin kis...

Mutane goma sha biyar, ciki har da ƴan jarida da ƴan siyasa suna fuskantar irin wannan zargi. Ofishin mai shigar da ƙara na Sudan ya zargi tsohon firaiministan ƙasar Abdalla Hamdok da laifin "tunzura" mutane domin su "yaƙi ƙasar" da kuma wasu laifuka da ka iya jawowa a yanke wa mutum hukuncin kisa, a cewar gidan talbijin na ƙasar Ofishin mai shigar da karar yana biyayya ga shugaban mulkin soji Janar Abdel Fattah al Burhan, wanda tun watan Afrilun 2023 dakarunsa suke gwabza yaƙi da na mataimakinsa kuma shugaban dakarun sa-kai na RSF, Mohamed Hamdan Dagalo. Mutane goma sha biyar, ciki har da ƴan jarida da ƴan siyasa, waɗanda su ma suke zaune a ƙasashen waje, suna fuskantar irin wannan zargi na "keta kundin tsarin mulki". Hamdok, wanda shi ne ɗan siyasa farar-hula mafi shahara a Sudan, ya rike muƙamin firaiministan ƙasar bayan tumɓuke gwamnatin Omar al Bashir.