Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Ana sa rai Trump zai yi sabbin naɗe-naɗe nan da ’yan kwanaki

Shugaban ma'aikatan da ke aiki da Biden ya buƙaci ma'aikatan da za su yi aiki da Trump su sanya hannu kan waɗansu takardun gwamnati da ake buƙata domin tabbatar da miƙa mulki cikin sauƙi. Ana sa rai zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump zai yi wasu muhimman naɗe-naɗe a sabon wa’adin mulkinsa na b...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:08
Ana sa rai Trump zai yi sabbin naɗe-naɗe nan da ’yan kwanaki
A taƙaice

Shugaban ma'aikatan da ke aiki da Biden ya buƙaci ma'aikatan da za su yi aiki da Trump su sanya hannu kan waɗansu takardun gwamnati da ake buƙata domin tabbatar da miƙa mulki cikin sauƙi. Ana sa rai zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump zai yi wasu muhimman naɗe-naɗe a sabon wa’adin mulkinsa na b...

Shugaban ma'aikatan da ke aiki da Biden ya buƙaci ma'aikatan da za su yi aiki da Trump su sanya hannu kan waɗansu takardun gwamnati da ake buƙata domin tabbatar da miƙa mulki cikin sauƙi. Ana sa rai zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump zai yi wasu muhimman naɗe-naɗe a sabon wa’adin mulkinsa na biyu, bayan wasu taruka da wasu da suka tsaya takara, kamar yadda kafafen yaɗa labarai suka bayyana. Shugaba Trump yana shirin yin wasu dokokin shugaban ƙasa da wasu sabbin tsare-tsare da dawo da wasu tsare-tsare da zarar ya shiga ofis wanda hakan yake nuni da yadda zai fara aiki gadan-gadan, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta CNN ta bayyana. Sannan ana sa rai galibin mutanen da ake sa rai za su samu manyan muƙamai za su halarci taron murnar nasarar da ya samu a garin Palm Beach da ke jihar Florida a ranar Talata kuma sun kammala shirye-shiryensu don kasancewa a wurin. Trump ya samu nasarar koma wa Fadar White House a ranar Laraba, inda ya samu fiye da kuri’u 270 na wakilan masu zabe kuma yanzu yana da kuri’u 295 yayin da ’yar takarar Democrat Mataimakiyar Shugaban Kasa Kamala Harris ta samu kuri’u 226, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya bayyana. Harris ta amsa shan kaye a wani jawabi da ta yi a Jami’ar Howard, wato jami’ar da ta yi karatu. Mataimakiyar Shugaban Kasar ta ce za ta ci gaba da gwagwarmaya don kawo ” ’yanci da damarmaki da adalci da kuma mutunta kowa da kowa. ”Shugaban Kasar Amurka mai barin gado Joe Biden ya yaba mata kan “gaskiyarta” da kuma “kwarin gwiwarta” a ranar Laraba bayan ’yar takarar Democrat wato Mataimakiyar Shugaban Kasar ta sha kayi a hannun dan takarar jam’iyyar Republican Donald Trump. “Abin da na gani a yau shi ne Kamala Harris din da na sani kuma nake matukar kauna. Ta kasance abokiyar tafiya ta kwarai kuma ta yi wa al’umma hidima da rikon gaskiya da kwarin gwiwa da kuma dabi’u masu kyau,” in ji Shugaba Biden kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa bayan Harris ta amsa shan kayi. Bayan bayyanar sakamakon zaben, Shugaba Biden ya kira Trump ta waya a ranar Laraba, inda ya gayyace shi Fadar White House saboda a fara shirye-shiryen mika mulki. Trump ya amsa gayyatar kuma hakan yana nuni da cewa za a mika mulki cikin lumana. “Shugaba Trump ya shirya zuwa ganawar, wadda za a yi nan kusa kuma ya yi godiya kan kiran shi da aka yi,” in ji daraktan yada labarai na kamfe din Trump Steven Cheung. Shugaban ma’aikatan Biden ya bukaci ɓangaren su Trump da su sanya hannu kan yarjejeniya kafin a fara shirye-shiryen miƙa mulkin, kamar yadda Fadar White House ta bayyana.