Rahotanni daga ƙasar sun ce tun daga misalin 7:00 na safe masu zanga-zangar suka soma taruwa inda suke riƙe da alluna waɗanda ke da rubutu game da wahalwalun da ake fama da su a ƙasar. Ƙungiyar Ƙwadago a Nijeriya ta soma gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar domin nuna rashin jin daɗi dangane da tsadar rayuwa da ake fama da ita a ƙasar. Ana gudanar da zanga-zangar ce duk da yunƙurin da gwamnatin tarayyar ƙasar ta yi na dakatar da ita. Haka kuma zanga-zangar ta biyo bayan wa’adin mako biyu da ƙungiyar ƙwadagon ta bai wa gwamnatin tarayyar ƙasar domin ta samar da matakai waɗanda za su rage tsadar rayuwa a ƙasar. Rahotanni daga ƙasar sun ce tun daga misalin 7:00 na safe masu zanga-zangar suka soma taruwa inda suke riƙe da alluna waɗanda ke da rubutu game da wahalwalun da ake fama da su a ƙasar. A Jihar Legas, masu zanga-zangar sun taru a Ikeja ƙarƙashin gada kuma rahotanni sun ce ɗumbin jama’a sun taru. A Jihar Oyo kuwa, mambobin na NLC sun taru a sakateriyar ƙungiyar da ke Agodi a Ibadan babban birnin jihar. A Kaduna ma haka abin yake inda mambobin ƙungiyar suka taru a sakateriyar ƙungiyar. Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun fito tun kimanin bakwai na safe. / Hoto: Reuters Raba ruwa da biskit Tun kafin soma wannan zanga-zanga, ƴan sandan Nijeriya sun ta jan kunnen masu niyyar fita zaga-zangar kan tayar da tarzoma. Sai dai a Jihar Legas, wani bidiyo da ya rinƙa yawo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda ƴan sandan suka rinƙa raba ruwa da biskit ga masu zanga-zangar. A cikin bidiyon, an ga yadda motar ƴan sandan ke ɗauke da robobi na ruwa da biskit inda ake bin motar a baya ƴan sandan na miƙa ruwan da biskit.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Ana gudanar da zanga-zangar 'tsadar rayuwa' a jihohin Nijeriya
Rahotanni daga ƙasar sun ce tun daga misalin 7:00 na safe masu zanga-zangar suka soma taruwa inda suke riƙe da alluna waɗanda ke da rubutu game da wahalwalun da ake fama da su a ƙasar. Ƙungiyar Ƙwadago a Nijeriya ta soma gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar domin nuna rashin jin daɗi dangane da t...

At a glance
Rahotanni daga ƙasar sun ce tun daga misalin 7:00 na safe masu zanga-zangar suka soma taruwa inda suke riƙe da alluna waɗanda ke da rubutu game da wahalwalun da ake fama da su a ƙasar. Ƙungiyar Ƙwadago a Nijeriya ta soma gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar domin nuna rashin jin daɗi dangane da t...
