Kawo zuwa yanzu ba a tabbatar da samun rasa rai ba, in ji kungiyar Red Cross ta Kenya. Ƙungiyar Bayar da Agaji ta red Cross a Kenya ta ce ma'aikatan ceto na ci gaba da ƙoƙarin ceton mutane da dama da zaftarewar ƙasa ta rutsa da su a yankin tsakiyar ƙasar sakamakon samun mamakon ruwan sama. Zaftarewar ƙasar ta afku a yankin Kimende, in ji sanarwar da Red Cross ta fitar ta shafin X. Ya zuwa yanzu ba a bayyana samun rasa rai ba sakamakon lamarin. Sanarwar ta ce "Jami'an tsaron sun yi wa yankin ƙawanya tare da ayyana shi a matsayin mai cike da hatsari." Mamakon ruwan sama da ambaliya na afku wa a ƙasar ta Gabashin Afirka tun ƙarshen watan Maris, inda ibtila'in ya yi ajalin aƙalla mutane 289 tare da raba 285,000 da matsugunansu A lamari mafi muni da ya afku, aƙalla mutane 61 ne suka mutu a karshen watan Afrilu, bayan zaftarewar ƙasa da ta biyo bayan ruwan sama a garin Mai Mahiu da ke tsakiyar Kenya.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Ana fargabar zaftarewar ƙasa ta rutsa da mutane da dama a Kenya
Kawo zuwa yanzu ba a tabbatar da samun rasa rai ba, in ji kungiyar Red Cross ta Kenya. Ƙungiyar Bayar da Agaji ta red Cross a Kenya ta ce ma'aikatan ceto na ci gaba da ƙoƙarin ceton mutane da dama da zaftarewar ƙasa ta rutsa da su a yankin tsakiyar ƙasar sakamakon samun mamakon ruwan sama. Zaftar...