Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Ana farautar waɗanda suka lalata mutum-mutumin shugaban Ghana

Gina mutum-mutumin Shugaba Nana Akufo-Addo ya janyo suka inda wasu ke cewa yabon kai ne. ‘Yan sanda a Ghana suna neman waɗanda ake zargi da hannu a lalata wani ɓangare na mutum-mutumin Shugaba mai barin gado, Nana Akufo-Addo, a Lardin Yammacin ƙasar. Aan lalata ƙafar hagun mutum-mutumin da aka gi...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:08
Ana farautar waɗanda suka lalata mutum-mutumin shugaban Ghana
De un vistazo

Gina mutum-mutumin Shugaba Nana Akufo-Addo ya janyo suka inda wasu ke cewa yabon kai ne. ‘Yan sanda a Ghana suna neman waɗanda ake zargi da hannu a lalata wani ɓangare na mutum-mutumin Shugaba mai barin gado, Nana Akufo-Addo, a Lardin Yammacin ƙasar. Aan lalata ƙafar hagun mutum-mutumin da aka gi...

Gina mutum-mutumin Shugaba Nana Akufo-Addo ya janyo suka inda wasu ke cewa yabon kai ne. ‘Yan sanda a Ghana suna neman waɗanda ake zargi da hannu a lalata wani ɓangare na mutum-mutumin Shugaba mai barin gado, Nana Akufo-Addo, a Lardin Yammacin ƙasar. Aan lalata ƙafar hagun mutum-mutumin da aka gina don tunawa da shugaban ƙasar kuma aka cire rubutun jikinsa, in ji wata sanarwar ‘yan sanda. "'Yan sanda suna yin ƙoƙarin ganin an kama waɗanda suka yi wannan aika-aikar domin gurfanar da su a gaban ƙuliya," in ji sanarwar. Shugaba Akufo-Addo ya fuskanci suka bayan ya ƙaddamar da mutum-mutumin a watan Nuwamba domin murnar cika alƙawuran da ya yi kafin ya hau ƙaragar mulki. An soke shi da yabon kai kuma rahotanni sun ce wasu mazauna yankin sun yi barazanar rusa mutum-mumin idan ya sauka daga kan mulki. Ƙarshen wa’ adi An lalata mutum-mutumin ne ranar Litinin da safe, kamar yadda rahotanni a kafafen watsa labaran Ghana suka ruwaito. Shugaban zai sauka daga kan mulki a watan Janairu bayan kammala wa’adi biyu na mulki. Ɗan takarar jam'iyyar hamayya kuma tsohon shugaban ƙasa John Mahama ne ya lashe zaɓen da aka gudanar a farkon wannan watan inda ya samu kusan kashi 57 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa- ratar nasara mafi yawa cikin sama da shekara 20. Za a rantsar da Mahama ranar 7 ga watan Janairu kuma ya yi alƙawarin bi da ƙasar sabuwar hanya.