Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Ana aikin ceto mutane bayan wata fashewa da ta rushe gine-gine a Ibadan

Ba a san dalilin da ya jawo fashewar ba, amma kafafen watsa labaran cikin gida sun rawaito cewa wasu gine-ginen sun rushe. Masu aikin ceto a Nijeriya na ci gaba da neman mutanen da suka ji rauni bayan wata fashewa da ta faru a birnin Ibadan na Jihar Oyo a ranar Talata da daddare, lamarin da ya ji...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:08
Ana aikin ceto mutane bayan wata fashewa da ta rushe gine-gine a Ibadan
At a glance

Ba a san dalilin da ya jawo fashewar ba, amma kafafen watsa labaran cikin gida sun rawaito cewa wasu gine-ginen sun rushe. Masu aikin ceto a Nijeriya na ci gaba da neman mutanen da suka ji rauni bayan wata fashewa da ta faru a birnin Ibadan na Jihar Oyo a ranar Talata da daddare, lamarin da ya ji...

Ba a san dalilin da ya jawo fashewar ba, amma kafafen watsa labaran cikin gida sun rawaito cewa wasu gine-ginen sun rushe. Masu aikin ceto a Nijeriya na ci gaba da neman mutanen da suka ji rauni bayan wata fashewa da ta faru a birnin Ibadan na Jihar Oyo a ranar Talata da daddare, lamarin da ya jijjiga gidaje tare da tsoratar da mutane har suka bazama kan tituna. Kawo yanzu dai ba a iya tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba, amma an garzaya da wadanda abin ya shafa asibiti, yayin da wasu mazauna garin suke maƙale a cikin ɓaraguzan gine-ginen da suka rutsa da su sakamakon tasirin fashewar. Ba a san dalilin da ya jawo fashewar ba, amma kafafen watsa labaran cikin gida sun rawaito cewa wasu gine-ginen sun rushe. An ji karar fashewar a birnin Ibadan mai nisan kilomita 130 daga birnin Legas. Wasu mazauna yankin sun ce ƙarfin fashewar ta sa tagogin gidajensu sun yi rugu-rugu “Hukumomin da abin ya shafa suna gudanar da aikin bincike da ceto a wurin da lamarin ya faru, an yi kira ga mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu saboda gwamnatin jihar Oyo na kan gaba wajen shawo kan lamarin,” in ji jihar Oyo a wata sanarwa da ta fitar. The state's commissioner for information Prince Dotun Oyelade earlier said "residents of Ibadan and immediate environ experienced an uncommon explosion about 8 p.m. (1900 GMT) this evening." Tun da fari, Kwamishinan watsa labarai na jihar Prince Dotun Oyelade ya ce "mazaunan Ibadan da kewaye sun ki ƙarar fashewar wani abu da ba a saba gani ba da misalin karfe 8 na dare (1900 GMT) da yammacin yau."