Kasar Turkiyya ta samu nasara da adadi mafi yawa na kuri'u 137 na kujerar neman matsayin da ya rage a kwamitin. An zabi Turkiyya a matsayin mamba a kwamitin adana kayan tarihi na Hukumar Raya Ilimi da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO a wa'adin shekarar 2023 zuwa 2027. An gudanar da zaben ne a ranar Laraba a babban taron kasashe mambobin da ke cikin kwamitin adana kayayyakin tarihi na duniya karo na 24 a birnin Paris. Turkiyya ta samu nasara da adadi mafi yawa na kuri'u 137 a bangaren kujerar neman matsayin da ya rage a kwamitin. Kasar ta taba aiki a kwamitin har sau biyu a shekarun 1983 zuwa 1989 da kuma shekarar 2013 zuwa 2017. A cewar ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya, ''kasar tana da burin amfani da gogewarta da ilimin da ta tara wajen gudanar da ayyuka da kare wurare 21 na kayayyakin tarihi a duniya da ke wakiltar duk wani ci-gaba da ya taba wanzuwa a yankin Anatolia tun zamanin da aka samu a fasaha tsakanin dan'adam kafin tarihi da aka fi sani da Neolithic, a ayyukanta da ta yi a duniya a matsayin mamba ta kwamitin UNESCO." Kwamitin tarihi na UNESCO, wanda ke da alhakin inganta al'adu da albarkatun kasa tare da tarihi a duniya wadanda ake la'akari da su a matsayin abubuwan da aka yi gadonsu kana kwamitin yana gudanar da ayyukan da suka shafi jerin abubuwan tarihi na duniya, inda wurare 21 daga Turkiyya suke daga ciki.
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
An zabi Turkiyya a matsayin mamba a kwamitin adana kayan tarihi na UNESCO
Kasar Turkiyya ta samu nasara da adadi mafi yawa na kuri'u 137 na kujerar neman matsayin da ya rage a kwamitin. An zabi Turkiyya a matsayin mamba a kwamitin adana kayan tarihi na Hukumar Raya Ilimi da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO a wa'adin shekarar 2023 zuwa 2027. An gudana...

Kasar Turkiyya ta samu nasara da adadi mafi yawa na kuri'u 137 na kujerar neman matsayin da ya rage a kwamitin. An zabi Turkiyya a matsayin mamba a kwamitin adana kayan tarihi na Hukumar Raya Ilimi da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO a wa'adin shekarar 2023 zuwa 2027. An gudana...
