Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

An yi musayar wuta tsakanin India da Pakistan a rana ta biyu a jere — Rundunar sojan Indiya.

Rundunar ta ce babu rahoton rasa rai, inda ta ce tana mayar da martani ne kan 'yan harbe-harbe da bindigogi "na ba gaira ba dalili". Sojojin Indiya da na Pakistan sun yi musayar harbe-harbe a daren jiya a kan layin iyaka da ya raba ƙasashen biyu a yankin Kashmir da ake taƙaddama a kai, a karo na...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:08
An yi musayar wuta tsakanin India da Pakistan a rana ta biyu a jere — Rundunar sojan Indiya.
Bu haberde ne var?

Rundunar ta ce babu rahoton rasa rai, inda ta ce tana mayar da martani ne kan 'yan harbe-harbe da bindigogi "na ba gaira ba dalili". Sojojin Indiya da na Pakistan sun yi musayar harbe-harbe a daren jiya a kan layin iyaka da ya raba ƙasashen biyu a yankin Kashmir da ake taƙaddama a kai, a karo na...

Rundunar ta ce babu rahoton rasa rai, inda ta ce tana mayar da martani ne kan 'yan harbe-harbe da bindigogi "na ba gaira ba dalili". Sojojin Indiya da na Pakistan sun yi musayar harbe-harbe a daren jiya a kan layin iyaka da ya raba ƙasashen biyu a yankin Kashmir da ake taƙaddama a kai, a karo na biyu a jere, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito, yana ambato rundunar sojin Indiya. Rundunar sojin Indiya ta ce an yi harbe-harben "na ba gaira ba dalili" daga wurare da dama na sojojin Pakistan "a tsawon layin iyaka a Kashmir" daga daren Asabar zuwa wayewar gari. "Sojojin Indiya sun mayar da martani yadda ya kamata da ƙananan makamai," in ji sanarwar. "Ba a samu rahoton asarar rai ba."