Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

An yi girgizar kasa mai karfin maki 5.2 a gabashin Turkiyya

Gwamnan Lardin Maltay da ke gabashin Turkiyya, inda girgizar kasa ta afku ya bayyana cewa an aike da jami'an agaji zuwa yankin, kuma ya zuwa wannan lokaci ba a samu labarin wata babbar arna ba. Girgizar kasa mai karfin maki 5.2 ta afku a Lardin Malatya na gabashin Turkiyya, in ji hukumar bayar da...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:08
An yi girgizar kasa mai karfin maki 5.2 a gabashin Turkiyya
A taƙaice

Gwamnan Lardin Maltay da ke gabashin Turkiyya, inda girgizar kasa ta afku ya bayyana cewa an aike da jami'an agaji zuwa yankin, kuma ya zuwa wannan lokaci ba a samu labarin wata babbar arna ba. Girgizar kasa mai karfin maki 5.2 ta afku a Lardin Malatya na gabashin Turkiyya, in ji hukumar bayar da...

Gwamnan Lardin Maltay da ke gabashin Turkiyya, inda girgizar kasa ta afku ya bayyana cewa an aike da jami'an agaji zuwa yankin, kuma ya zuwa wannan lokaci ba a samu labarin wata babbar arna ba. Girgizar kasa mai karfin maki 5.2 ta afku a Lardin Malatya na gabashin Turkiyya, in ji hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar. Hukumar Yaki da Annoba da Bayar da Agajin Gaggawa ta Turkiyya (AFAD) a ranar Alhamis din nan ta bayyana cewa girgizar ta afku a gundumar Battalgazi a karkashin kasa da zurfin kilomita 13,93 da misalin karfe 1604 agogon Turkiyya (1304GMT). An ji motsin girgizar kasar a largunan da ke kewaye da lardin Malatya. Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Anadolu, Gwamnan Malatya Ersin Yazici ya ce "Ba mu samu labarin wani mummunan abu ba. Jami'anmu na ci gaba da aiki a yankin." Bayan afkuwar girgizar kasar, Ministan Harkokin Cikin Gidan Turkiyya Ali Yerlikaya ya ce ba a samu rahoton samun wata barna ba sakamakon ibtila'in, kuma an kai jami'an don bincike da gano ko akwai wata matsala da ka iya afkuwa. Bayanai kan girgizar kasar - Karfin maki 5.2 - Zurfin kilomita 13.93 - Babu rahoton wata ɓarna ko asarar rai - Tawagogin agaji na cikin shirin ko ta kwana