Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

An yanke wa Imran Khan da matarsa hukuncin zaman gidan yari na shekara 14

Wannan hukuncin na zuwa kwana guda bayan wata kotu ta yanke wa Imran Khan hukuncin zaman gidan yari na shekara goma. An yanke wa tsohon Firaiministan Pakistan Imran Khan da matarsa hukuncin zaman gidan yari na shekara 14 kan samun su da laifin sayar kadarorin ƙasar ba bisa ƙa’ida ba, kamar yadda...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:08
An yanke wa Imran Khan da matarsa hukuncin zaman gidan yari na shekara 14
De un vistazo

Wannan hukuncin na zuwa kwana guda bayan wata kotu ta yanke wa Imran Khan hukuncin zaman gidan yari na shekara goma. An yanke wa tsohon Firaiministan Pakistan Imran Khan da matarsa hukuncin zaman gidan yari na shekara 14 kan samun su da laifin sayar kadarorin ƙasar ba bisa ƙa’ida ba, kamar yadda...

Wannan hukuncin na zuwa kwana guda bayan wata kotu ta yanke wa Imran Khan hukuncin zaman gidan yari na shekara goma. An yanke wa tsohon Firaiministan Pakistan Imran Khan da matarsa hukuncin zaman gidan yari na shekara 14 kan samun su da laifin sayar kadarorin ƙasar ba bisa ƙa’ida ba, kamar yadda jaridar Dawn ta ruwaito. Hukuncin da kotun ta yanke a Islamabad na zuwa ne kwana ɗaya bayan an yanke wa Khan hukuncin zaman gidan yari na shekara 10, mako guda kafin babban zaɓen ƙasar. Haka kuma wata kotu ta yanke wa Khan hukuncin zaman gidan yari na shekara uku kan sayar da kayayyakin ƙasar waɗanda suka kai sama da rupee miliyan 140 a lokacin da yake minista tsakanin 2018 zuwa 2022. Duk da cewa daga baya an dakatar da hukuncin, amma Khan na tsare sakamakon zarginsa da hannu a wasu laifukan. Sai dai Khan ya kafe kan cewa ya sayi kadarorin ne bisa ƙa’ida. Jami’an gwamnati suna zargin mataimakan Khan sun sayar da kyaututtukan ne a Dubai.