Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

An wayi gari da ƙarar harbe-harben bindiga a Kinshasa

Rahotanni daga babban birnin Jamhuriyar Kongo na cewa wasu mutane sanye da kayan sojoji sun kai farmaki gidan wani babban ɗan siyasar ƙasar a kusa da fadar shugaban ƙasa, lamarin da ya jawo asarar rayuka. An ji ƙarar harbe-harben bindiga a babban birnin Kongo da safiyar Lahadi inda wasu mutane ɗa...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:08
An wayi gari da ƙarar harbe-harben bindiga a Kinshasa
Kwa muhtasari

Rahotanni daga babban birnin Jamhuriyar Kongo na cewa wasu mutane sanye da kayan sojoji sun kai farmaki gidan wani babban ɗan siyasar ƙasar a kusa da fadar shugaban ƙasa, lamarin da ya jawo asarar rayuka. An ji ƙarar harbe-harben bindiga a babban birnin Kongo da safiyar Lahadi inda wasu mutane ɗa...

Rahotanni daga babban birnin Jamhuriyar Kongo na cewa wasu mutane sanye da kayan sojoji sun kai farmaki gidan wani babban ɗan siyasar ƙasar a kusa da fadar shugaban ƙasa, lamarin da ya jawo asarar rayuka. An ji ƙarar harbe-harben bindiga a babban birnin Kongo da safiyar Lahadi inda wasu mutane ɗauke da bindiga sanye da kayan sojoji suka yi arangama da masu tsaron wani babban ɗan siyasar ƙasar a kusa da fadar shugaban ƙasa. Rahotanni sun tabbatar da cewa aƙalla mutum uku suka rasa rayukansu sakamakon rikicin, kamar yadda mai magana da yawun ɗan siyasar ya tabbatar wa kafafen watsa labarai na ƙasar. Mutanen ɗauke da makamai sun far wa gidan Vital Kamerhe da ke Kinshasa, dan majalisar tarayya kuma tsohon mataimakin firaministan tattalin arziki, amma jami’an tsaronsa sun yi ba-ta-kashi da su, kamar yadda Michel Moto Muhima ya bayyana a shafinsa na X, wanda shi ne kakakinsa. Kafofin yada labaran cikin gida sun bayyana mutanen a matsayin sojojin Congo. Sai dai ba a bayyana ko suna kokarin kama dan siyasar ba, wanda dan takarar shugaban majalisar dokokin kasar Congo ne a zaben da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar din da ta gabata, amma aka samu jinkiri sakamakon takaddamar cikin gida ta jam'iyya mai mulki a ƙasar.