Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Ɗan ƙunar-baƙin-wake ya kashe mutum 11 a Mogadishu babban birnin Somalia

Mutumin ya tayar da bam ɗin ne a daidai lokacin da wasu matasa masu neman shiga aikin soja suka yi jerin-gwano a wajen wani sansanin soji a Mogadishu. Akalla mutum 11 sun rasa rayukansu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wani ɗan ƙunar-baƙin-wake ya tayar da bam a wajen wani sansanin soja a babb...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:08
Ɗan ƙunar-baƙin-wake ya kashe mutum 11 a Mogadishu babban birnin Somalia
Bu haberde ne var?

Mutumin ya tayar da bam ɗin ne a daidai lokacin da wasu matasa masu neman shiga aikin soja suka yi jerin-gwano a wajen wani sansanin soji a Mogadishu. Akalla mutum 11 sun rasa rayukansu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wani ɗan ƙunar-baƙin-wake ya tayar da bam a wajen wani sansanin soja a babb...

Mutumin ya tayar da bam ɗin ne a daidai lokacin da wasu matasa masu neman shiga aikin soja suka yi jerin-gwano a wajen wani sansanin soji a Mogadishu. Akalla mutum 11 sun rasa rayukansu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wani ɗan ƙunar-baƙin-wake ya tayar da bam a wajen wani sansanin soja a babban birnin Somaliya, Mogadishu, a ranar Lahadi, in ji wani jami'i. Harin ya faru ne a sansanin sojojin Somaliya na Damaanyo da ke unguwar Hodan, inda aka kai wa matasa masu neman shiga aikin soja hari yayin da suke jerin-gwano a wajen ginin. Wani jami'in tsaro daga unguwar Warta Nabada da ke kusa da wurin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa fararen hula biyu da wasu masu neman shiga aikin soja na daga cikin waɗanda suka mutu a harin. Ya ce an kai waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci. Kungiyar ta'addanci mai alaka da Al-Qaeda, al-Shabaab, ta ɗauki alhakin kai harin. Al-Shabaab ta shafe fiye da shekara 16 tana yakar gwamnatin Somaliya, kuma sau da yawa tana kai hare-hare kan jami'an gwamnati da sojoji.