Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

An tura masu zanga-zanga 632 da ake tuhuma da sata a Kano gidan yari

Tun da fari babban mai shigar da ƙarar na ma'aikatar shari'a Salisu Tahir ya yi zargin cewa mutanen sun aikata laifukan ne a ranar 1 ga watan Agusta inda suka kutsa tare da ɓaranata kayayyakin gwamnati da na al'umma a jihar. Wata kotun tafi-da-gidanka ta Jihar Kano ta ba da umarnin aika masu zang...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:08
An tura masu zanga-zanga 632 da ake tuhuma da sata a Kano gidan yari
Em resumo

Tun da fari babban mai shigar da ƙarar na ma'aikatar shari'a Salisu Tahir ya yi zargin cewa mutanen sun aikata laifukan ne a ranar 1 ga watan Agusta inda suka kutsa tare da ɓaranata kayayyakin gwamnati da na al'umma a jihar. Wata kotun tafi-da-gidanka ta Jihar Kano ta ba da umarnin aika masu zang...

Tun da fari babban mai shigar da ƙarar na ma'aikatar shari'a Salisu Tahir ya yi zargin cewa mutanen sun aikata laifukan ne a ranar 1 ga watan Agusta inda suka kutsa tare da ɓaranata kayayyakin gwamnati da na al'umma a jihar. Wata kotun tafi-da-gidanka ta Jihar Kano ta ba da umarnin aika masu zanga-zanga 632 gidan gyaran hali bisa tuhumarsu da sace-sace da ɓarnata kayayyakin al'umma da na gwamnati a ranar farko ta zanga-zangar da aka yi. Ana tuhumar mutanen da laifuka bakwai da suka hada da kitsa aikata mugayen laifuka da sace-sace da taruwa ba bisa doka ba da tunzura tashin hankali da shiga wurare ba tare da izini ba da kuma tayar da wuta. Kotun ta ɗage zaman kotun har sai ranar 19 ga watan Agusta don cigaba da sauraron ƙarar. Tun da fari babban mai shigar da ƙarar na ma'aikatar shari'a Salisu Tahir ya yi zargin cewa mutanen sun aikata laifukan ne a ranar 1 ga watan Agusta inda suka kutsa tare da ɓaranata kayayyakin gwamnati da na al'umma a jihar. Wasu waɗanda ake tuhumar sun amsa laifukansu yayin da sauran suka musanta tuhume-tuhumen. Atoni Janar na Jihar Haruna Isa-Dederi ya ce gwamnati ta samar da kotunan tafi-da-gidanka har uku don gurfanar da waɗanda ake zargin, kuma za a yi nazarin shari'ar kafin zama na gaba.