Sakamakon farko-farko ya nuna Bassirou Diomaye Faye ne kan gaba a zaɓen shugaban ƙasa na Senegal. Tsohon Firaministan Senegal ya amsa shan kaye a hannun ɗan takarar jam'iyyar adawa a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ƙasar, kamar yadda sakamakon farko-farko na zaɓen ke nunawa, kwana ɗaya bayan kammala kaɗa ƙuri'a. Amadou Ba, ɗan takarar jam'iyya mai mulki ya faɗa a wata sanarwa daga ofishin kamfe ɗinsa ranar Litinin, cewa yana taya murna ga ɗan takarar jam'iyyar adawa, Bassirou Diomaye Diakhar Faye, kuma yana masa fatan alheri. Nasarar da ya samu a zagayen farko na zaɓen ta dace da abin da aka gani na yadda mutanen ƙasar ke nuna ɓacin-ransu da rashin aikin-yi da shugabanci nagari a ƙasar da ke Yammacin Afirka. Diomaye Faye, wanda ke da goyon baya daga shahararren ɗan adawa Ousmane Sonko, ya sha alwashin raba Senegal da rashawa a ɓangaren gwamnati. Watannin tararrabi Zaɓen da ya gudana ranar Lahadi ya biyo bayan watannin da aka kwashe ana tararrabi da rashin zaman lafiya bayan da shugaba mai ci, Macky Sall ya yi yunƙurin dakatar da zaɓe har zuwa ƙarshen shekara. Zanga-zangar da ta biyo bayan yunƙurin ta girgiza kyakkyawan sunan da Senegal take da shi a matsayin tsayayyiyar ƙasar dimukurɗiyya a yankin da ya sha fama da jerin juyin mulki a ƴan shekarun nan.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Ɗan takarar jam'iyya mai mulki a Senegal ya amsa shan kaye a zaɓen shugaban ƙasa
Sakamakon farko-farko ya nuna Bassirou Diomaye Faye ne kan gaba a zaɓen shugaban ƙasa na Senegal. Tsohon Firaministan Senegal ya amsa shan kaye a hannun ɗan takarar jam'iyyar adawa a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ƙasar, kamar yadda sakamakon farko-farko na zaɓen ke nunawa, kwana ɗaya bayan...

Sakamakon farko-farko ya nuna Bassirou Diomaye Faye ne kan gaba a zaɓen shugaban ƙasa na Senegal. Tsohon Firaministan Senegal ya amsa shan kaye a hannun ɗan takarar jam'iyyar adawa a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ƙasar, kamar yadda sakamakon farko-farko na zaɓen ke nunawa, kwana ɗaya bayan...
