Yaƙin ya kuma raba mutane fiye da mutum miliyan shida da muhallansu a cikin kasar, yayin da sama da miliyan guda suka yi hijira zuwa kasashen waje, akasarinsu zuwa kasashen Chadi da Masar da ke makwabtaka da kasar. Ma’aikacin bayar da agaji na Sudan Shakir Elhassan da iyalinsa na daga cikin miliyoyin mutanen da aka tilasta musu barin gidajensu bayan da yaƙi ya ɓarke a Sudan a shekarar da ta gabata. Bayan watanni goma, yana daga cikin da dama waɗanda suke gargadi kan cewa za a iya faɗawa cikin wani irin bala’i na yunwa a ƙasar. “Buƙatun ba su da iyaka,” kamar yadda manajan watsa labarai na Care International ya bayyana, inda ya jaddada yadda cewa ƙasashen duniya sun ƙi mayar da hankali kan lamarin. Yaƙi ya ɓarke a watan Afrilun bara tsakanin Shugaban Sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma Mohamed Hamdan Daglo wanda shi ne shugaban rundunar RSF. Elhassan ya tsere daga Khartoum babban birnin ƙasar a watan Yuli, inda ya samu matarsa da ƴaƴansa uku waɗanda tuni dama suka nemi mafaka a birnin Wad Madani mai nisan kilomita 180 daga Khartoum. Sai dai a watan Disambar bara, RSF ta kai hari jihar Jazirah, wadda ta zama wata mafaka ga masu gudun hijira a yankin. “Lamari ne mai ban tsoro, na tsere daga Jazirah da tufafi ɗaya kaɗai a baya na,” in ji shi. “A kan hanya, akwai dubban mutane da ke tafiya a ƙafa, inda suke cikin fargaba. Akasarinsu mata ne da yara.” Shi da iyalansa sun samu matsuguni kilomita 400 daga gashin birnin, a babban birnin lardin Kassala kusa da iyakar Sudan da Eritrea, inda a nan suka zauna kuma ya ce akwai da dama waɗanda ke ci gaba da zuwa wurin neman mafaka. ‘Dubbai sun rasu, miliyoyi sun rasa muhallansu’ Yakin da ake yi a Sudan ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane, ciki har da mutane 10,000 zuwa 15,000 a garin El Geneina kaɗai wanda ke yammacin yankin Darfur, a cewar alkaluman Majalisar Ɗinkin Duniya. Yaƙin ya kuma raba mutane fiye da mutum miliyan shida da muhallansu a cikin kasar, yayin da sama da miliyan guda suka yi hijira zuwa kasashen waje, akasarinsu zuwa kasashen Chadi da Masar da ke makwabtaka da kasar. Majalisar Dinkin Duniya ta ce ɓarkewar cututtuka na kara yin barazana, musamman a wuraren da ake fama da cunkoson jama’a, inda tuni kasar ke fuskantar ɓarkewar cutar kwalara da zazzabin dengue. A cikin kasar, mutum miliyan 25 - fiye da rabin al'ummar kasar - na bukatar agajin jin kai. Daga cikin su, miliyan 18 na fuskantar matsala ko matsananciyar yunwa. William Carter, wanda shi ne daraktan hukumar ƴan gudun hijira ta ƙasar Norway a Sudan ya kai ziyara Darfur a ƴan makonnin nan. “Baya ga zautuwa da kuma asarar da aka tafka, abin da ke damuna shi irin yunwar da ake fama da ita,” in ji shi. “Mutane sun sayar da komai nasu. Gidajen burodi ba su samar da rabin abin da suke samarwa sakamakon ƙarancin fulawa ko alkama.” “Tsaka mai wuya” A farkon watan Fabrairu, ƙungiyar likitoci ta Doctors Without Borders (MSF) ta yi gargaɗi kan cewa yaro ɗaya na mutuwa a duk bayan awa biyu a sansanin gudun hijira na Zamzam da ke Arewacin Darfur. Wannan na nufin yara 13 na mutuwa a kullum, inda akwai da dama da ke cikin fargabar faɗawa cikin halin yunwa. Clementine Nkweta-Salami, jami'ar MDD mai kula da ayyukan jin kai a Sudan, a watan Nuwamba, ta yi gargadin cewa take hakkin bil'adama a Darfur "zallan mugunta ce", tana mai bayyana yaran a matsayin "waɗanda suka shiga tsaka mai wuya" inda ta ce an yi wa mata fyaɗe a gaban iyayensu mata. Deepmala Mahla, shugabar kula da ayyukan jin kai na Care International, ta ce kasar na cikin barazanar rasa duka ahalinta”. “Yawancin yara suna daf da mutuwa saboda yunwa,” in ji ta. Alice Verrier, daga kungiyar agaji ta Premiere Urgence Internationale ta Faransa, ta ce kawo yanzu agajin jin kai da ake aika wa kasar ta Afirka ba shi da yawa idan aka kwatanta da Ukraine bayan da Rasha ta mamaye kasar a shekarar 2022. Ta ce, "Idan aka duba makudan kudaden da aka ware wa Ukraine, ko kadan ba ma a kan ma'auni daya muke ba." "An manta da rikicin Sudan gaba daya."
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Ƴan Sudan na gargaɗi kan 'matsananciyar yunwa' da tsananin buƙatar jin kai
Yaƙin ya kuma raba mutane fiye da mutum miliyan shida da muhallansu a cikin kasar, yayin da sama da miliyan guda suka yi hijira zuwa kasashen waje, akasarinsu zuwa kasashen Chadi da Masar da ke makwabtaka da kasar. Ma’aikacin bayar da agaji na Sudan Shakir Elhassan da iyalinsa na daga cikin miliy...

Yaƙin ya kuma raba mutane fiye da mutum miliyan shida da muhallansu a cikin kasar, yayin da sama da miliyan guda suka yi hijira zuwa kasashen waje, akasarinsu zuwa kasashen Chadi da Masar da ke makwabtaka da kasar. Ma’aikacin bayar da agaji na Sudan Shakir Elhassan da iyalinsa na daga cikin miliy...
